Da Dumi-Dumi: An kashe kwamishina, Rabe Nasir, a gidansa da ke Katsina
1 - tsawon mintuna
- Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kutsa gidan kwamishinar Fasaha da Kimiyya na Jihar Katsina sun halaka shi
- Majiyoyi sun tabbatar da cewa 'yan bindigan sun kutsa gidan Dr Rabe Nasir ne bayan sallar la'asar suka bindige shi
- Kafin ya zama kwamishina, Rabe Nasir ya taba rike mukamin mashawarcin Gwamna Aminu Bello Masari kan Kimiyya da Fasaha
Jihar Katsina - An yi wa kwamishinan Kimiyya da Fasaha na jihar Katsina, Dokta Rabe Nasir kisar glla.
Daily Trust ta rahoto cewa an bindige shi ne a gidansa da ke Fatima Shema Estate da ke birnin Katsina.
Wata majiya wacce ta tabbatar da lamarin ta ce:
"An bindige marigayi Nasir ne bayan sallar La'asar a gidansa da ke nan Fatima Shema Estate."
Marigayi Nasir ne mashawarci na musamman ga Gwamna Aminu Bello Masari kan Kimiyya da Fasaha kafin a nada shi Kwamishina.
Amma da Daily Trust ta ziyarci gidansa, wani mutum, da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce tun daren jiya aka kashe shi.
Ya ce:
"An daba masa wuta ne a cikinsa a yayin da ya ke zaune a falonsa sannan aka ja gawarsa zuwa bandaki aka rufe."
An haife shi ne a garin Mani da ke karamar hukumar Mani na jihar Katsina.
Ku dakaci karin bayani ...
Asali: Legit.ng
Tags: