Akwai Abin Tsoro Da Takaici A Kasar Nan, Malamai dai sun yi nasu kokarin: Dr Rabiu Rijiyar Lemo

Akwai Abin Tsoro Da Takaici A Kasar Nan, Malamai dai sun yi nasu kokarin: Dr Rabiu Rijiyar Lemo

  • Sheikh Muhammad Rabi'u Rijiyar Lemo ya yi kira ga shugabanni su farka daga baccinsu
  • Malamin yace dole ne wadanda Allah ya dorawa nauyin shugabancin su tsayar da wannan barna
  • A farkon makon nan, yan bindiga sun babbaka matafiya akalla 20 a jihar Sokoto da ransu

Babban Malamin addinin Islama kuma Lakcara a kwalejin ilimi dake Gumel a jihar Jigawa, Dr Rabiu Rijiyar Lemo ya yi tsokaci kan kisan gillan da ake yiwa yan Najeriya kulli yaumin.

Dr Rijiyar Lemo ya bayyana cewa ya zama wajibi Shugabanni su tashi tsaye wajen kare rayukan jama'arsu tare da hukunta masu aikata wannan laifi.

A jawabin da ya daura a shafinsa na Facebook, Malamin yace wadanda Allah ya daurawa hakkin jama'a su sauke hakkin da ke kansu.

A cewarsa:

Kara karanta wannan

Ana yi wa Shugaban kasa martani a kan zuwa Legas, ana makokin mutum 80 a Sokoto

"Babu shakka halin da kasar nan take ciki na rashin tsaro da zubar da jinin bayin Allah wadanda ba su ji ba, ba su gani ba, da cin mutuncinsu da salwantar da dukiyarsu abin tsoro ne da Takaici matuka, kuma wajibi ne a kan wadanda Allah ya dorawa nauyin shugabancin wannan al'umma su yi duk abin da za su iya don tsayar da wannan barna.
Wajibi ne shugabanni su farka daga barcin da suke yi, su hukunta duk wani mai hannu a cikin wannan barna, koda kuwa ta hanyar kashe duk wanda aka kama da hannu cikin wannan ta'asa. ne, kuma a yayata hukuncin kowa ya ji kuma ya gani."

Dr Rabiu Rijiyar Lemo
Akwai Abin Tsoro Da Takaici A Kasar Nan, Malamai dai sun yi nasu kokarin: Dr Rabiu Rijiyar Lemo Hoto: Muhammad Rabi'u Rijiyar Lemo
Asali: Facebook

Ya kara da cewa Malaman addini wanda ya hada da Limamai da masu wa'azi sun yi fadakarwa sau tari kan yadda za'a magance matsalar tsaron.

Kara karanta wannan

Dalilin da yasa muka haramta shan Shisha a jihar Kano, Yusuf Ibrahim Lajawa

Hakazalika ya yi kira ga jama'a su cika da tsoron Allah don a samu saukin lamarin

Yace:

"Allah shaida ne malamai da masu wa'azi da dama sun gabatar da hudubobi da Jan hankali a lokuta daban daban don ganin an kawo karshen wannan barnar.
Wajibi ne a kanmu gaba daya mu koma zuwa ga Allah, mu kaskantar da kanmu don neman yaye mana wannan hali da muke ciki."

An kashe mana mutum 80 a dare 1 – Manyan Sokoto sun aikawa Buhari wasika mai ban tausayi

Manyan mutanen garin Sabon Birni a karkashin kungiyar Gobir Development Association sun aikawa shugaba Muhammadu Buhari takarda.

Jaridar Daily Trust tace kungiyar Gobir Development Association ta sanar da mai girma shugaban kasa ne irin kisan kiyashin da ake yi wa mutanen Sabon Birni.

A wasikar ta su, dattawan jihar sun bayyana cewa hankalinsu ya tashi, babu wani katabus a tare da su, bayan zaluncin da aka yi masu kamar dai yadda aka saba.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya yiwa sojojin da suka raunata a yaki da ISWAP abin alheri na kudade

Da suke bayani a takardar a ranar Laraba, 8 ga watan Disamba, 2021, kungiyar tace yan bindiga sun addabi yankin Isa, Sabon Birni da Goronyo da bangaren Shinkafi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Tags: