Ku shirya, ba zamu biya kudin albashin Disamba da wuri ba: Gwamnati ga ma'aikata

Ku shirya, ba zamu biya kudin albashin Disamba da wuri ba: Gwamnati ga ma'aikata

  • Gwamnatin tarayya ta ankarar da daukacin ma'aikatanta cewa albashin Disamba fa akwai 'kura
  • Shugabar ma'aikatan gwamnatin Najeriya ta gargadi ma'aikata su bi a hankali wajen kashe albashin Nuwamba da aka biyasu
  • Jami'an yan sandan Najeriya kuwa da alamun abin ya ritsa da su har yanzu basu samu albashin Nuwamba ba

Abuja - Gwamnatin tarayya ta baiwa ma'aikatanta shawara su bi da sannu wajen kashe albashinsu na Nuwamba saboda akwai yiwuwan jinkirin biyan na Disamba, 2021.

Shugabar ma'aikatan gwamnatin tarayya, Dr Folasade Yemi-Esan, ta bayyana hakan a takardar da ta saki ranar Asabar, Thisday ta ruwaito.

Ta ce ma'aikata su shirya cin Kirismeti da albashin Nuwamba saboda matsalolin da ake fuskanta na kudin shiga ya shafi kudin albashin ma'aikata.

Kara karanta wannan

Uwargida ta waskawa miji mari ana tsakiyar shirin ma'aurata a gidan Rediyo, bidiyo

Shugabar ma'aikata
Ku shirya, ba zamu biya kudin albashin Disamba da wuri ba: Gwamnati ga ma'aikata Hoto: Presidency
Asali: Facebook

Takardar mai dauke da kwanan wata 25, Nuwamba, 2021, ya samu rattafa hannun Dr. S.A. Adegoke a madadin Shugabar ma'aikatan.

Wani sashen takardan yace:

"Ku sani cewa duk da wannan shawara da muka bada, muna tabbatarwa ma'aikata za'ayi iyakar kokari wajen ganin ba'a samu jinkiri ba."
"Amma dai a dau wannan shawara da gasken gaske."

Yan sanda sun shiga damuwa bayan jin shuru na albashin Nuwamba

Jami’an ‘yan sandan Najeriya har yanzu ba su samu albashin watan Nuwamba ba, sakamakon zargi kan wasu ma’aikatan ma’aikatar kudi, kasafin kudi da tsare-tsare ta kasa suka yi na gudanar da biyan kudaden.

Dangane da wannan al’amari, hukumar ‘yan sanda ta kai dauki domin kwantar da tarzoma daga wanda ke korafin rashin biyansu albashi mako guda kenan a watan Disamba.

Punch ta tattaro cewa ‘yan sanda yawanci suna karbar albashi ne a ranar 25 ga kowane wata amma abin da ya faru a yanzu na kara haifar da damuwa a cikin ‘yan sandan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng