Karbe wayar Sowore ta jawowa Jami’an DSS matsala a kotu, Alkali yace su biya shi N2m

Karbe wayar Sowore ta jawowa Jami’an DSS matsala a kotu, Alkali yace su biya shi N2m

  • Jami’an DSS sun karbe waya da kudin Omoyele Sowore a lokacin da za su kama shi a otel a 2019
  • 'Dan gwagwarmayar ya kalubalanci jami’an tsaro, kuma ya yi nasara inda Alkali tace a biya shi N2m
  • Alkalin tace ya kamata DSS ta nemi izini daga kotu kafin a karbe duk wasu kayan da ke hannunsa

Abuja - Babban kotun tarayya da ke zama a garin Abuja ta umarci hukumar jami’an tsaro masu fararen kaya su biya Naira miliyan biyu ga Omoyele Sowore.

Jaridar Premium Times tace Alkalin babban kotun tarayyar ta ci DSS wannan tara ne a dalilin karbar wayar Yele Sowore tun a 2019 ba tare da bin doka ba.

Alkalin da ta ke sauraron wannan shari’a, Anwuli Chikere ta ba DSS umarni su gaggauta fitowa Sowore da wayar sa kirar iPhone da kudin da suka karbe masa.

Kara karanta wannan

An gurfanar da mutumin da aka kama da ATM 2,863 a Legas

Mai shari’a Anwuli Chikere tace jami’an tsaron sun karbe wannan waya da N10, 000 daga hannun wanda ake tuhuma ne ba tare da sun samu izini daga kotu ba.

Ba a bi doka ba - Alkali

A hukuncin da ta zartar, Chikere ta bayyana kwacen da aka yi wa ‘dan jaridar da wanda ta saba doka, haramtacciya, kuma ta keta hakkinsa na zama ‘dan kasa.

The Nation tace Alkali tace DSS ba za ta fake da cewa ta karbe kayan na wani ‘dan gajeren lokaci ba ne domin abin ya faru ne tun shekaru biyu da suka wuce.

Soworeyace su biya shi N2m
Mista Yele Sowore Hoto: Nigeria-Diaspora-International-Movement
Asali: Facebook

Bugu da kari, Alkali mai shari’a ta bukaci DSS ta ba wanda ta ke karar hakuri. An nemi hukumar ta buga wannan ne a manyan jaridu biyu nan da watanni biyu.

Kara karanta wannan

Babbar magana: 'Yan sanda sun shiga damuwa bayan jin shuru na albashin Nuwamba

A lokacin da abin ya faru, jami’an DSS sun ce sun karbe wayar Sowore wanda ya jagoranci zanga-zangar #RevolutionNow ne domin ana yin wasu bincike a kansu.

Lauyan da ya tsayawa ‘dan takarar shugaban kasar a zaben 2019, Femi Falana ya ji dadin wannan hukunci da aka yanke, yace gaskiya ta samu nasara a shari’ar.

Da ake shari’a a kotu, wani lauyan DSS ya fadawa Alkali cewa wayar Omoyele Sowore ta fada hannun jami’an tsaro ne, ba wai karbe su aka yi daga wajensa ba.

Amma Falana SAN ya kalubalanci wannan ikirari, yace babu wanda yake da hurumin yin haka ba tare da takarda da ta bada damar bincike daga gaban Alkali ba.

Da Buhari gara babu - Shehi

Shi kuma Sheikh Bello Yabo, an ji ya na cewa ko ba a fadawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba, ya san cewa ya ci amanar al’umma, domin ya gaza kare jama'a.

Kara karanta wannan

Alkali ya dawo da Birgediya Janar din da aka kora daga gidan Soja shekarun da suka wuce

Malamin yace hukuncin kisa aka yanke masu a kan Buhari, amma mulkin na sa bai tsinana masu komai ba, yace har za a iya cewa gara a zauna babu masu iko.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng