Alkali ya dawo da Birgediya Janar din da aka kora daga gidan Soja shekarun da suka wuce
- Kotun ma’aikata da ke zama a birnin Abuja ta yanke hukunci a shari’ar ASH Sa’ad da sojojin kasa
- A 2016 aka kori Birgediya Janar A.S.H. Sa’ad da wasu sojojin daga aiki, aka yi masu ritayar dole
- Alkali yace wannan ritaya da aka yi wa Janar A.S.H. Sa’ad ta saba doka, ya ce a biya shi albashinsa
Abuja - Kotun ma’aikata da ke zama a birnin tarayya, ta umarci sojojin kasa su dawo da wani babban jami’insu da suka sallama daga aiki a shekarar 2016.
Premium Times ta fitar da rahoto cewa Birgediya Janar A.S.H. Sa’ad (mai ritaya), ya samu nasara a kotun da ke Abuja a ranar Talata, 7 ga watan Disamba, 2021.
Janar A.S.H. Sa’ad ya na cikin wadanda aka kora daga aiki tare da wasu jami’ai 37 a wancan lokaci.
Da yake zartar da hukunci a jiya, Alkali mai shari’a Benedict Kanyip yace wanda ya kawo kara ya iya tabbatar da gaskiyar cewa an kore shi ba tare da hakki ba.
Tsohon sojan ya shaidawa kotu cewa ba a bi dokar aiki wajen sallamar shi da abokan aikinsa ba, yace ba ayi wani bincike kafin ayi waje da su daga gidan soja ba.
Hukuncin da Alkali ya zartar
Benedict Kanyip yace babu yadda za ayi a ce an yi wa Sa’ad ritayar dole domin ba a tabbatar da ya aikata wani laifi ba, amma ba a yarda a kara masa matsayi ba.
A hukuncinsa, Alkalin ya ce ba za a iya dawo da Janar A.S.H. Sa’ad (mai ritaya) bakin aiki ba saboda ya kamata ace ya yi ritaya daga aiki tun a shekarar 2019.
Rahoton yace kotu tayi fatali da rokon Janar Sa’ad, inda yace ya kamata shi ma ya zama Manjo Janar kamar yadda abokan karatunsa suka zama kafin su yi ritaya.
“Yi wa wanda ya shigar da kara ritaya a 9 ga watan Yuni, 2016 ya sabawa doka da tsarin aikin gidan soja, saboda haka ritayar ba ta yi ba.”
“Wanda ake tuhuma zai maida wanda ya kawo kara aiki a matsayinsa na Birgediya Janar, a biya shi albashinsa har zuwa 2019.” - Benedict Kanyip.
NLC za ta yi ta da gwamnati
Kungiyar NLC ta bayyana abin da ta ke shirin yi muddin aka kara farashin man fetur. Shugaban NLC na kasa, Kwamred Ayuba Wabba ne ya ja kunnen gwamnati.
NLC tace karin albashin da aka yi zai zama a banza idan litar man fetur ya zama N340. Shugaban NLC ya ba gwamnatin tarayya zabi uku, yace ta daina biyewa IMF.
Asali: Legit.ng