Aisha Buhari, BUA, Indimi da Gambari za su samu kyautar digirin Dakta daga jami’ar Arewa
- Jami’ar KWASU da ke garin Malete za ta yaye daliban da suka kammala karatun digirorinsu a 2021
- Shugaban Jami’ar, Farfesa Muhammed Akanbi yace za a karrama wasu manya a wajen wannan biki
- Daga cikinsu akwai Aisha Buhari, Ibrahim Gambari, Mohammed Indimi da Alhaji Abdulsamad Rabiu
Kwara - Mai dakin shugaban Najeriya, Aisha Muhammadu Buhari da Farfesa Ibrahim Gambari su na cikin wadanda za su samu karramawa da digirin dakta.
Jaridar Punch ta ce jami’ar jihar Kwara da ke garin Malete za ta karrama uwar gidar shugaban kasa, Aisha Muhammadu Buhari da digir-digir watau dakta.
Haka zalika shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari zai samu irin wannan karramawa a wajen bikin yaye daliban da za ayi.
Shugaban jami’ar KWASU, Farfesa Muhammed Akanbi, SAN, ya shaidawa manema labarai wannan a ranar Litinin, 6 ga watan Disamba, 2021 a Ilorin.
Farfesa Muhammed Akanbi, SAN yace mutane bakwai aka zaba za a ba wannan digiri a bikin yaye dalibai da za ayi a ranar Asabar 11 ga watan Disamba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sauran wadanda za su samu Daktar kyauta
Aisha Buhari za ta samu digiri a fannin kasuwanci, shi kuma Gambari wanda shi ne zai shugaban farko mai kula da jami’ar zai samu mafi koluwar digirin dakta.
Sauran wadanda za a karrama da digirin sun hada da Mohammadu Indimi a bangaren fasaha, sai Alh. Abdulsamad Rabiu wanda zai samu digirin kasuwanci.
Akanbi yace Jolayemi Omotowa za ta samu digirin dakta a fannin kimiyya, sai kuma Injiniya Bamidele Adewumi wanda za a ba digiri a sha’anin fasaha.
Da yake bayani, jaridar Today ta fitar da rahoto cewa an ji jami’ar ta KWASU ta kori dalibai 87 tsakanin 2019 da 2021 saboda an same su da aikata laifuffuka.
Farfesan yace dalibai 6, 620 za a yaye da suka kammala digiri a bikin da za a yi na bana, sannan akwai wasu 417 da suka gama karatun digirgir da digirdigir.
Aisha Buhari tayi kira ga 'yan jarida
Kwanaki aka ji cewa matar shugaban ƙasa, Aisha Muhammadu Buhari, ta na kira ga kafafen watsa labarai su rika bibiyar ayyukan alherin matan gwamnoni.
Aisha Buhari wanda ta kasance bakuwa ta musamman a wajen wani taro da aka yi tayi wannan jawabi ne ta bakin Aliyu Abdullahi, wanda ya wakilce ta a zaman.
Asali: Legit.ng