Shekara 1 da janye dogon yajin-aiki, akwai yiwuwar a sake rufe jami’o’in gwamnati a Najeriya
- Wa’adin da kungiyar malaman jami’a ta ba gwamnatin tarayya ya kare a ranar Lahadin da ta wuce
- Har wannan wa’adi na kwanaki 21 suka shude, ba a iya biyawa malaman jami'an bukatun na su ba
- Shugaban kungiyar ASUU na kasa yace alkawari daya gwamnatin kasar ta cika a shekara daya
Abuja - Gwamnatin tarayya ta na kokarin dakatar da malaman jami’a daga zuwa aiki yayin da wa’adin da aka ba ta ya cika karshen makon da ya wuce.
Kungiyar ASUU ta ba gwamnatin Najeriya tsawon makonni uku domin a biya mata bukatunta domin a gujewa yajin aiki, a jiya wannan wa’adi ya shude.
Punch tace tayi hira da karamin Ministan ilmi, Chukwuemeka Nwajiuba, ya shaida mata sun rubuta takarda sun nemi a biya malaman jami’a alawus dinsu.
Amma shugabannin ASUU sun bayyana cewa har yanzu bukata daya kacal aka biya masu a cikin jeringiyar bukatun da aka amince da su kafin su koma aiki.
Shugaban ASUU na kasa, Emmanuel Osodeke ya koka da cewa duk da sun gana da Dr Chris Ngige, har yanzu ba a cika alkawuran da aka yi masu a bara ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Alkawuran da aka yi wa ASUU
Gwamnatin tarayya tayi alkawarin za ta saki N30bn domin farfado da jami’o’i. Baya ga haka an yi alkawarin za a biya N22.1bn a matsayin alawus din ma’aikata.
Baya ga haka akwai batun dakatar da amfani da IPPIS wajen biyan malamai albashi, biya bashin kudin karin matsayi da suka makale da sake duba yarjejeniyar 2009.
ASUU ta ce har yanzu ta ji shiru
Da ‘yan jarida suka tuntubi Farfesa Osodeke a lokacin su na taro ranar Asabar, 4 ga watan Disamba, 2021, yace ba a cika masu alkawuran da aka dauka ba.
“Wa’adin zai kare a ranar Lahadi. Bukata daya suka biya mana; Kudin farfado da jami’o’i, shi ma N20bn suka biya jami’o’i. Ba a cika sauran ba.”
“Jami’anmu za su yi taro gobe, za mu sanar da ku matsayar wannan zama a gobe (Lahadi) – Osodeke.
ASUU za ta koma yajin aiki?
Watanni uku da suka wuce ne aka ji cewa kungiyar malaman jami’a sun bayyana shirinsu na shiga wani sabon yajin-aiki, karo na biyu a cikin shekaru biyu.
Hakan na zuwa ne bayan an rufe jami’o’i a kwanaki idan aka yi kusan shekara ba ayi karatu ba.
Asali: Legit.ng