Da Ɗumi-Ɗumi: Tsohon Babban Hafsan Sojojin Ƙasa Na Najeriya, Janar Wushishi, Ya Rasu

Da Ɗumi-Ɗumi: Tsohon Babban Hafsan Sojojin Ƙasa Na Najeriya, Janar Wushishi, Ya Rasu

  • Rundunar sojojin Najeriya ta shiga zaman makoki bayan sanarwar rasuwar Janar Mohammed Inuwa Wushishi
  • Wushishi, ya yi aiki a matsayin babban hafsan sojojin kasa na Najeriya daga Oktoban 1981 zuwa Oktoban 1983, a zamanin Jamhuriya ta biyu a Kasar
  • Tsohon babban hafsan sojojin da aka haifa a karamar hukumar Wushishi, jihar Neja ya rasu ne a wani asibiti a Landan yana da shekaru 81

Tsohon Babban Hafsan Sojojin Kasa na Najeriya a zamanin jamhuriya ta biyu, Janar Mohammed Inuwa Wushishi ya riga mu gidan gaskiya.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa majiyoyi daga 'yan uwansa sun ce yana wani asibiti ne a Landan yana da shekaru 81 a duniya.

Ya rasu ya bar mata daya, Kande Muhammadu Wushishi da 'ya'ya bakwai ciki har da tsohon Kwamishinan Saka Hannun Jari a Jihar Neja, Honarabul Kabiru Muhammadu Wushishi.

Kara karanta wannan

An tura dakarun Sojoji Najeriya kasar Mali don tabbatar da zaman lafiya

Da Dumi-Dumi: Tsohon Babban Hafsan Sojojin Kasa Na Najeriya, Janar Wushishi, Ya Rasu
Tsohon Babban Hafsan Sojojin Kasa Na Najeriya, Janar Wushishi, Ya Rasu a Landan. Photo credit: Terry Abdul-Kareem Zekeri, Khamis Musa Muhammad Read
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ita ma ta tabbatar da rasuwarsa inda ta rahoto cewa tsohon shugaban sojin ya rasu ne a yammacin ranar Asabar a Landan inda aka masa magani kan wata cuta da ya dade yana fama.

An haifi shi ne a garin Wushishi, Jihar Neja, sannan Mr Wushishi ya yi aiki a matsayin babban hafsan sojojin kasa daga watan Oktoban 1981 zuwa 1983.

Ya kuma taba rike mukamin babban kwamandan, GOC 4 na sojojin kasa, a rundunar sojojin Najeriya a 1976 kuma Shugaban Kwallejin Horas Da Jami'an Sojoji ta Jaji a 1979.

Rasuwar Wushishi babban rashi ne ga Najeriya, Gwamnan Neja

Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello a martanin da ya yi game da rasuwar Wushishi ya ce muturwarsa babban rashi ne ga jihar ta ma kasa baki daya.

Bello, cikin sanarwar da babban sakataren watsa labaransa, Mary Noel Berje, ta fitar ya ce gwamnati da al'ummar jihar sun yi jimamin rasuwar tsohon shugaban sojojin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164