Da duminsa: Gwamnati ta bukaci wadanda sukayi rigakafin Korona sau 2 su je a kara musu na 3
- Kamar yadda akeyi a Amurka da sauran kasashen waje, za'a fara alluran Korona na uku a Najeriya
- Kawo yanzu kimanin yan Najeriya milyan bakwai suka yi allurarsu ta farko na rigakafin ta Korona
- An fara hana ma'aikatan Gwamnati shiga ofis sai an tsira musu allurar rigakafin
FCT Abuja - Gwamnatin tarayya ta yi kira ga wadanda aka yiwa rigakafin Korona sau biyu su je a kara musu na uku saboda tabbatar da tsaro da lafiya.
Kakakin hukumar cigaban kananan asibitoci NPHCDA, Mohammed Ohitoto, a bayyana hakan ranar Juma'a, rahoton TheCable.
A cewar jawabin, duk wadanda suka dade da yin rigakafin su garzaya asibitoci don yin na uku fari daga ranar Juma'a, 10 ga Disamba, 2021.
Jawabin yace kwamitin fadar shugaban kasa na yaki da annobar Korona tare da hadin kan ma'aikatar kafia ta amince da a fara baiwa mutane allura ta uku ga wanda yayi allurai biyu na rigakafin AstraZeneca, Moderna, Pfizer Bio-N-Tech ko akkura daya na 1 Johnson & Johnson.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ga wani ballin jawabin:
"Shugaban hukumar NPHCDA, Dr Faisal Shuaib ya ce sharadin yiwa mutumin allura na uku shine ya kasance mai shekaru 18 da abinda yayi sama kuma akwai takazarar watanni shida da yin rigakafi na biyu na AstraZeneca, Moderna ko Pfizer Bio-N-Tech, ko kuma tazarar watanni da yin na J&J."
A cewar hukumar NPHCDA, yan Najeriya 6,887,362 sun yi allurarsu ta farko yayinda yan Najeriya 3,720,695 suka yi allurai biyu kawo ranar 2 ga Disamba.
An hana ma'aikatan gwamnati shiga ofis don basu yi rigakafin Korona ba
Jami'an tsaro sun hana ma'aikatan gwamnatin da ba suyi rigakafin Korona ba shiga ofishoshinsu a sakatariyar gwamnati dake birnin tarayya Abuja, rahoton Punch.
Wadanda basu yi rigakafin ba amma suka gabatar da takardar shaidar gwajin Korona PCR da ya nuna basu da cutar zasu shiga.
Kungiyar ma'aikatan gwamnatin tarayya ta yi kira ga Gwamnati ta dage wannan doka zuwa watan Maris 2022.
A riwayar ChannelsTV, misalin karfe 7 na safe jami'an tsaro suka mamaye kofar shiga sakatariyar gwamnati kuma suka bukaci kowa ya nuna hujjar cewar yayi rigakafi ko bai da Korona.
Asali: Legit.ng