An gurfanar da matar da ta yi asubanci ta sace N2.5m cikin asusu a gidan wani mutum

An gurfanar da matar da ta yi asubanci ta sace N2.5m cikin asusu a gidan wani mutum

  • An gurfanar da wata mata, Foluke Olubu a gaban kuliya kan zarginta da sace asusu tare da Naira miliyan 2.5 ciki
  • Wacce ake zargin mai shekaru 32 ta musanta aikata laifin bayan an karanto mata tuhumar a gaban kotu
  • Alkalin kotun ta bada belin wacce aka gurfanar din kan kudi N500,000 tare da gabatar da tsayayyu biyu masu kwakwarar sana'a

Jihar Legas - An gurfanar da wata mata mai shekaru 32, Foluke Olubu, a gaban kotun Majistare da ke Ikeja kan zarginta da sace asusu dauke da zunzurutun kudi Naira miliyan 2.5, rahoton The Nation.

Olubu, wacce aka gurfanar a ranar Juma'a, ba tare da bayyana adireshinta ba tana fuskantar tuhumar aikata sata sai dai ta musanta tuhumar da ake mata.

An gurfanar da matar da ta yi asubanci ta sace asusu da N2.5m a cikinsa
Matar da ake tuhuma da sace asusu tare da N2.5m ta gurfana a kotu. Hoto: The Nation
Asali: Twitter

Kara karanta wannan

An gurfanar da wata mata a kotu kan satar katin waya na N1m

Mai gabatar da karar, Sufeta Christopher John, ya ce asusun na wani Mr Kingsley Odimegwu ne.

John ya shaida wa kotu cewa wacce aka yi karar ta aikata laifin ne a ranar 8 ga watan Oktoba misalin karfe 5.30 na safe a Taiwo Street da ke Mafoluku a Oshofi, Jihar Legas.

An bada belin Olubu kan kudi N500,000

Alkalin kotun, Mrs KA Ariyo, ta bada belin wacce ake zargin kan kudi N500,000 tare da gabatar da tsayayun mutane biyu kamar yadda ya zo a ruwayar The Nation.

Ariyo ta bada umurnin cewa tsayayyun mutanen su kasance masu sana'a kwakwara sannan su gabatar da shaidan biyan haraji ga gwamnatin jihar Legas na shekaru biyu.

Kotun ta dage cigaba da sauraron shari'ar har zuwa ranar 10 ga watan Janairun shekarar 2022.

Laifin sata dai ya ci karo da sashi na 287 na dokar masu laifi na jihar Legas ta shekarar 2015, kuma ana iya yanke wa wanda aka samu da laifin har shekaru uku a gidan gyaran hali.

Kara karanta wannan

Akwai yiwuwar Kotu ta sake sakin jagoran kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu a zaman shari’ar yau

Kotu ta ɗaure wani matashi da ya yi asubanci ya tafi coci ya sace kujerun roba

A wani rahoton, wata kotun majistare ta daure wani matashi, Lekan Alaka, mai shekaru 19, watanni 3 bisa satar kujerun roba masu kimar N91,200 daga cocin Mount Zion Angelican.

‘Yan sandan sun kama Alaka da laifin sata kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Alkali Olajumoke Somefun ya yanke hukunci bisa tabbatar da laifin da ya aikata bisa ruwayar Vanguard.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164