Kwamitin majalisar dattawa: A kowacce shekara ana shigo da shinkafa mai nauyin 2mt

Kwamitin majalisar dattawa: A kowacce shekara ana shigo da shinkafa mai nauyin 2mt

  • Kwamitin majalisar dattawa mai kula da harkokin noma ya ce a kowacce shekara ana sumogal din 2mt na shinkafa
  • Kwamitin ya sanar da cewa, ana cin shinkafa mai nauyin metric tan miliyan 6.7 a kowacce shekara amma 5 metric tan miliyan ake nomawa
  • Sanata Enagi, mataimakin shugaban kwamitin ya ce suna son a kafa hukumar noman shinkafa a Najeriya domin a saka wasu dokoki da za su gyara harkar

FCT, Abuja - Kwamitin majalisar dattawa kan aikin noma ya ce ana shigo da shinkafa a kalla metric tan miliyan biyu ta sumogal a kowacce shekara a kasar nan, TheCable ta ruwaito.

A yayin jawabi a wani taron masu ruwa da tsaki a Abuja a ranar Laraba, Muhammad Enagi, mataimakin shugaban kwamitin, ya ce shinkafar sumogal ta na daga cikin shinkafa metric tan 6.7 da ake ci a kaowacce shekara a kasar nan.

Kara karanta wannan

Fannin shari'ar kasar nan ba zai sassauta ba sai ya ga bayan rashawa, CJN Tanko

Kwamitin majalisar dattawa: A kowacce shekara ana shigo da shinkafa mai nauyin 2mt
Kwamitin majalisar dattawa: A kowacce shekara ana shigo da shinkafa mai nauyin 2mt. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Kungiyar United Nations Development Programme (UNDP)–Global Environment Facility (GEF tare da hadin guiwar Women Farmers Advancement Network (WOFAN) ne suka hada taron.

TheCable ta ruwaito cewa, Enagi ya ce yawan shinkafar da ake samarwa a kasar nan ta kai metric tan 3.7 miliyan a shekarar 2017 zuwa metric tan 5 miliyan a shekarar 2021.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Duk da haka, ana cin shinkafa metric tan 6.7 miliyan a kowacce shekara a Najeriya, hakan ne ke kawo gibin da dole sai an shigo da metric tan miliyan 2 cikin kasar nan," Sanatan yace.

Dan majalisar ya ce a halin yanzu ya mika bukata gaban majalisar ta samar da hukumar habaka noman shinkafa ta Najeriya domin a kafa ta.

Ya ce idan aka amince da bukatar, za a samar da tsarin aiki da na shugabanci wanda zai fitar da darajar shinkafa. Za a kuma tsara yadda manoman shinkafa za su dinga gyarata, cashewa, cire tsakuwa da kuma siyar da ita.

Kara karanta wannan

Ayyuka 257 aka kwafo daga kasafin kudin 2021 masu darajar N20bn, ICPC

"A yadda muke samar da shinkafa, ya dace a ce Najeriya ta na da hukumar habaka noman shinkafa ta kasa da kuma gamsasshen tsarin da za mu yi amfani da shi wurin dogaro da kanmu wurin saman da shinkafar ci har da ta fitarwa waje," sanatan yace.
“A gaskiya masana'antun samar da shinkafa ta Najeriya kara zube suke domin kuwa babu tsari wurin ayyukansu.
“Muna da kungiyoyi kamar su Paddy Rice Dealers Association of Nigeria (PRIDAN), Rice Farmers Association of Nigeria (RIMAN) da sauransu," ya kara da cewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng