A rika tallafawa matan da suka rasa Mazajensu da marasa karfi, Gwamnan Gombe

A rika tallafawa matan da suka rasa Mazajensu da marasa karfi, Gwamnan Gombe

  • Gwamnan jihar Gombe ya bayyana muhimmancin taimakawa matan da suka rasa mazajensu
  • Gwamnan ya bayyana muhimmancin taimakawa matan yan sandan da aka kashe a faggen fama
  • Taron ya samu halartar uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari da Sufeto Janar na ‘yan sanda

Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na Jihar Gombe ya jaddada muhimmancin tallafawa matan da suka rasa mazajensu da suka rasu da iyalan jami'an tsaro da suka mutu a bakin aiki.

Gwamna Inuwa Yahaya ya yi wannan jawabi ne a safiyar Alhamis, yayin kaddamar da wani littafi wanda Hajiya Hassana Abubakar ta rubuta a karkashin kungiyar matan 'yan sanda, POWA.

Ismaila Uba Misilli Babban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamnan Jihar Gombe ya bayyana hakan a jawabin da ya saki.

A cewarsa, taron ya samu halartar uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, wacce ta samu wakilcin Mrs Lauretta Onochie da Sufeto Janar na ‘yan sanda, Usman Baba Alkali.

Kara karanta wannan

An gano abin da Buhari ya fadawa Shugaban kasar Afrika ta Kudu kafin ya lula zuwa Dubai

Hakazalika gwamnonin jihohin Kebbi da Neja da suka samu wakilci da 'yan majalisar tarayya da sarakunan gargajiya da sauran fitattun mutane.

Gwamna Inuwa, ya bukaci Al ummah da su ci gaba da kula da baiwa matan da mazajensu suka rasu fifiko a yayin ayyukansu dama sauran marasa galihu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A rika tallafawa matan da suka rasa Mazajensu da sauran marasa karfi, Gwamna Inuwa
A rika tallafawa matan da suka rasa Mazajensu da sauran marasa karfi, Gwamna Inuwa Hoto: Isma'il Uba Misilli
Asali: Facebook

Yace:

“Nazo wannan taro da kaina ne don nuna goyon baya ga POWA, da ‘yan sandan Najeriya musamman ga dan uwana kuma abokina sufeta janar na yan sandan Najeriya, wanda na san shi tun 1982 muke abota tare da wani abokin mu, Lamido Ahmed, wanda yanzu ya rasu, don haka wannan taron zai bamu damar taimakawa domin ni da Babban Sifeta mun yi rashin aboki, masoyi wanda ya rasu ya bar iyalai".
“Kun san a cikin al’ummar mu, al’adu, addini a wasu bangarori kuma al’amuran da suka shafi al’umma galibi suna haifar da damuwa ga matan da suka rasa mazajensu, amma a matsayin mu na masu imani dole ne mu tashi tsaye wajen sauke nauyin daya rataya a wuyan mu don taimakawa wajen rage wahalhalu gare su da ’ya’yansu.”

Kara karanta wannan

Ganduje ya yi magana kan daliban Islamiyya 20 da suka mutu a hatsarin jirgin ruwa a Kano

Ya kuma yabawa marubuciyar, Hajiya Hassana Abubakar, wacce ita ma ta rasa mijinta kuma tana da ‘ya’ya tara bisa yadda ta fito da matsalolin marasa aure a cikin al’umma da kuma bayyana irin tallafi na musamman da suke bukata dama baiwa jama’a damar yin tunani da nazari a kan su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng