Jirgin yakin Super Tucano ya yi raga-raga da maboyar manyan makaman ISWAP, ya hallaka kwamandojin su

Jirgin yakin Super Tucano ya yi raga-raga da maboyar manyan makaman ISWAP, ya hallaka kwamandojin su

  • Jirgin yakin Super Tucano ya lalata babban maɓoyar makaman kungiyar ta'addancin ISWAP da sansanin ɗaukar horon su
  • Rahotanni sun bayyana cewa jirgin yaƙin ya hallaka manyan gawurtattun kwamandojin su yayin harin a Tafkin Chadi
  • Dakarun sojojin sun kuma samu nasarar kashe mayakan ISWAP da yawan gaske, waɗan da ke wurin a lokacin harin

Sabon jirgin yaki kirar Super Tucano na rundunar sojin ƙasar nan ya lalata maɓoyar makaman kungiyar ISWAP da kuma sansanin ɗaukar horon su a tafkin Chadi.

Daily Nigerian ta rahoto cewa wasu daga cikin yan ta'addan dake wurin sun zarce lahira yayin ruwan bama-bamai a lokuta daban-daban da sojin Operation Hadin kai suka aiwatar a Kayowa, Tumbum Jaki da Tumbun Akawu na yankin.

Super Tucano
Jirgin yakin Super Tucano ya yi raga-raga da maboyar manyan makaman ISWAP, ya hallaka kwamandojin su Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Yayin harin ta sama da ƙasa ranar Talata, sojojin sun gano wurin da ake ikirarin shine Hedkwatar kungiyar ISWAP, wanda ya ƙunshi kwamandojinsu, mayaƙa da maɓoyar makamansu.

Kara karanta wannan

Sojoji sun sheke dan IPOB yayin da tsagerun ke kokarin sace likitoci a jihar Imo

Wata majiya daga cikin jami'an sojin, ya shaida wa PRNigeria cewa dakarun sojin sun kaddamar da harin ne bayan gano yan ta'addan na tattaruwa a yankin tafkin Chadi.

Jami'in yace:

"Jami'an sashin Fasaha suka fara bada rahoton wurin, da irin ayyukan da ake a wurin."
"Yayin harin da sojoji suka kai, sun gano cewa sun ji karar fashe-fashen abubuwa, wanda hakan ya tabbatar da cewa akwai kayayyakin haɗa bama-bamai a wurin."

Yan ta'adda nawa sojojin suka kashe?

Jami'in ya kara da cewa a binciken da aka yi na farko, sojojin sun gano cewa harin ya hallaka manyan gawurtattun kwamandojin yan ta'addan.

"A binciken nasarar da muka yi a harin na farko, mun gano cewa harin ya hallaka gawutattun kwamandojin yan ta'addan, da kuma mayakan su da yawan gaske."

Kara karanta wannan

Ana cikin gwabzawa, Mayakan ISWAP suka tarwatse yayin da suka hangi jirgin yakin Super Tucano na shawagi

A wani labarin na daban kuma Sojoji sun hallaka yan ta'adda 90, sun damke kasurgumi da suke nema ruwa a jallo

Hedkwatar tsaro ta bayyana nasarorin da dakarun soji suka samu a yankin arewa maso gabashin Najeriya cikin mako biyu.

Daraktan watsa labarai na HQ, Bernard Onyeuko, yace sojojin sun hallaka aƙalla yan ta'adda 90, sun kame wasu 21.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262