Da duminsa: Shugaba Muhammadu Buhari ya dira birnin Dubai
- Shugaban kasa ya samu rakiyar ministoci kimanin mutum 10, Ministan tsaro da kuma sauran jami'an gwamnati
- Shugaba Buhari zai gana da manyan Sarakunan kasar UAE tare da Babban Hafsan Sojin kasar
UAE - Shugaba Muhammadu Buhari ya dira birnin Dubai, haddadiyar daular Larabawa da daren Laraba domin halartan taron baja kolin EXPO 2020.
Wannan taron baja koli zai auku ne ranar Juma'a, 3 ga watan Disamban 2021.
Hadimin shugaban kasa, Buhari Sallau, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki kuma Legit ta samu.
Shugaban zai samu rakiyar ministoci da jami'an gwamnati sama da 10.
Shugaba Buhari zai gana da Sarkin Dubai, Sheikh Mohammed bin Rashid Al Maktoum, da kuma Yarima mai jiran gadon masarautar Abu Dhabi Mohamed bin Zayed Al Nahyan.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Da wa zai tafi?
Adesina ya ce Buhari zai samu rakiyar Ministoci 10 da wasu mukarrabansa
Ga jerinsu:
1. Ministan harkokin waje Geoffrey Onyeama;
2. Ministan masana'antu, kasuwanci da zuba hannun jar, Otunba Adeniyi;
3. Ministar Kudi, Hajia Zainab Shamsuna;
4. Ministan Noma da cigaban karkara, Dr Mouhammad Abubakar.
5. Ministan Sufurin sama, Hadi Sirika;
6. Ministan Lafiya, Dr Osagie Ehanire;
7. Ministan Sadarwa, Dr Isa Ali Pantami;
8. Ministan karafuna da ma'adinai, Olamilekan Adegbite;
9. Karamar ministan zuba jari, Amb Maryam Katagum.
10. Ministan Tsaro, Bashir Salihi Magashi;
11. NSA Babagana Monguno;
12. Dirkata Janar na NIA, Amb Ahmed Rufa'i Abubakar
13. Shugabar hukumar yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa.
Asali: Legit.ng