Akwai yiwuwar Kotu ta sake sakin jagoran kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu a zaman shari’ar yau
- Ana jita-jitar cewa yau za a sake zama a kotu domin a fito da shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu
- Idan hakan ta tabbata, za a bada belin Nnamdi Kanu wanda ya taba tserewa da aka bada belin shi a baya
- Kafin yanzu kotu ta ce sai watan Junairun 2022 za a sake zama da Kanu a shari’arsa da gwamnati
FCT, Abuja - Nnamdi Kanu, jagoran kungiyar IPOB mai fafatukar kafa kasar Biyafara da ke tsare, na iya samun beli a yau, Alhamis, 2 ga watan Disamba, 2021.
Rahotanni daga PM News sun bayyana cewa babu mamaki a bada belin Mazi Nnamdi Kanu yau.
Wani lauyan gwamnatin Najeriya ne ya bayyana wannan kamar yadda jaridar nan ta Sahara Reporters ta fara bayyana wannan rahoto a ranar Larabar nan.
Sai dai har yanzu babu tabbacin wannan kishin-kishin da ake ji. Haka zalika babban lauyan da ya tsayawa Kanu a kotu, bai iya tabbatar da wannan maganar ba.
Da jaridar PM News ta tuntubi lauyan Nnamadi Kanu, Barista Ifeanyi Ejiofor, ba a same shi ba. Amma Aloy Ejimakor esq yace akwai zaman da za ayi a yau.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Shi ma Barista Aloy Ejimakor ya na cikin wadanda suke kare Kanu a shari’arsa da gwamnatin Najeriya a wani babban kotun tarayya da ke zama a garin Abuja.
A ranar 12 ga watan Nuwamban 2021 ne aka zauna a kotu na karshe da shugaban na kungiyar IPOB, inda lauyoyinsa su ka yi bore, har aka daga kara sai 2022.
Ana neman alfarma wajen Buhari
Tun daga nan dattawan kasar Ibo suke ta shiga da fita domin ganin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarni a janye wannan shari’a da aka yi a kotu.
Shugaba Muhammadu Buhari yace wannan roko ya yi masa nauyi, amma zai duba. Sai dai a doka, bai halatta shugaban kasa ya tsoma baki a harkar shari’a ba.
Jaridar Sahara Reporters tace za ayi zaman na musamman a kotu a ranar Alhamis, inda a nan za a samu damar fito da Kanu a karon farko tun da aka dawo da shi gida.
Idan an bada belinsa a yau, ba zai zama na farko ba domin kotu ta taba sakin shi a 2017, amma ya tsere.
Ban aikata laifi ba - Kanu
Kwanaki aka ji yadda aka gurfanar da Nnamdi Kanu a gaban babbar kotun tarayya a Abuja a kan wasu zargi bakwai da gwamnatin tarayya ta ke tuhumarsa da su.
Da yaka kare kan shi a kotu a gaban Alkali, Mazi Kanu ya musanta zargin da ake yi masa. Daga ciki ana tuhumarsa da laifin cin amanar kasa da kuma ta'addanci.
Asali: Legit.ng