Sanatoci sun kaure da cacar baki kan rashin adalci a daukar ma'aikata a rundunar soji

Sanatoci sun kaure da cacar baki kan rashin adalci a daukar ma'aikata a rundunar soji

  • An samu sabani tsakanin wasu sanatoci kan batun daukar ma'aikata a rundunar sojojin Najeriya na kwanan nan
  • Wasu sanatoci sun tado da batun rashin adalci a atisayen daukar ma'aikatan, inda suka nemi a yi karin haske akai
  • Sai dai, mai jagorantar zaman ya dage kan cewa, ba zaman da ake yi ba kenan, kuma ba za a yi batun a zaman ba

Abuja - Jaridar Leadership ta ruwaito cewa, a jiya ne Sanatoci suka shiga cacar baki akan tsari da kuma yadda aka gudanar da atisayen daukar sojoji a kasar nan.

A yayin wani taron kwamitin majalisar dattawa kan sojoji, an yi ta samun zarge-zarge da cece-kuce kan rashin gaskiya a cikin atisayen daukar aikin da sojojin Najeriya suka yi a baya-bayan nan.

Ganawar wani zaman tattaunawa ne da kwamitin ya yi da kwamanda na horo da koyarwa na rundunar sojojin Najeriya, Manjo Janar S.O Olabanji.

Kara karanta wannan

An tura dakarun Sojoji Najeriya kasar Mali don tabbatar da zaman lafiya

Sanatocin Najeriya
Sanatoci sun kaure da cacar baki kan rashin adalci a daukar ma'aikata a rundunar soji | Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Wani mamba a kwamitin kuma mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Abdullahi Ibrahim Danbaba a zaman majalisar ya zargi Manjo Janar Olabanji da karkatar da aikin daukar sojoji da rundunar ta yi kwanan nan.

Sai dai shugaban riko na kwamitin, Sanata Abba Moro wanda ya jagoranci zaman majalisar, ya ce Danbaba bai kyauta ba, yana mai cewa, “wannan taron ba na irin wannan bincike ba ne."

Wani a kwamitin, Sanata Barinada Mpigi, ya fusata da wannan lamarin, ya sake tayar da batun, inda ya ce “batun daukar ma’aikata ba batun da za a yi watsi da shi ba ne ko kuma a yanke hukunci a kansa."

Sanata Moro ya sake jaddada rashin amincewa da yin batun inda ya jaddada cewa zaman ba wai na duba batun daukar ma’aikata da sojoji suka yi ba ne, batu ne kan horar da dabaru ga jami'ai.

Kara karanta wannan

Akwai yiwuwar Kotu ta sake sakin jagoran kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu a zaman shari’ar yau

A cewarsa:

“Tambayoyin da abokan aikina ke yi kan zargin da ake yi na daukar ma’aikata ana jefa su ga wanda bai dace ba. Shugaban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Farouk Yahaya shine wanda zai iya yin adalci akan irin wadannan zarge-zarge ko bincike."

Basu gamsu da dagewar da Abba Moro ya yi na cewa bai kamata a yi tambayoyin daukar ma'aikata a zaman ba, sai Sanata Danbaba da Mpigi suka fice daga taron a fusace.

Danbaba ya bayyana fushinsa ga ‘yan jarida kan abin da ya wakana a zaman majalisar, ya ce ya fice daga ganawar da Sanata Mpigi ne bisa matakin kama-karya da Sanata Moro ya dauka, kamar yadda jaridar Independent ta ruwaito.

Sanatoci sun nemi a karawa 'yan NYSC kudin alawus din abinci

A wani labarin, kwamitin majalisar dattawa mai kula da harkokin wasanni da ci gaban matasa ya bayar da shawarar karin kudin ciyar da 'yan NYSC a kullum daga Naira 600 ga kowane mutum zuwa N1,000, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

An dakatad da Likita da Malamar jinya da aka kama suna lalata cikin asibiti

Shugaban kwamitin Obinna Ogba, ya yi wannan roko ne a ranar Talata yayin da yake gabatar da rahoton kwamitinsa kan kasafin kudin 2022 ga kwamitin kasafin kudi.

Kwamitin majalisar dattawa mai kula da harkokin cikin gida a watan da ya gabata ya kara yawan alawus din ciyar da fursunonin da ke tsare a gidajen yari daga N450 zuwa Naira 1,000 a kowacce rana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Tags: