Buhari ya tabbatarwa 'yan Najeriya zaman makoki a kasar na daf da zuwa karshe
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan 'yan sanda biyu da wasu yan ta'adda a Kudu maso Gabas suka kashe
- Shugaban kasar ya bawa 'yan Nigeria tabbacin cewa nan da kankanin lokaci zaman makoki da ake yi a kasar zai zo karshe
- Shugaba Buhari ya yi addu'ar Allah ya jikan dukkan wadanda suka rasu a yankunan da ake fama da rashin tsaro kuma ya bawa iyalansu hakurin rashi
FCT, Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya bawa yan Najeriya tabbacin cewa nan ba da dadewa ba za'a samu zaman lafiya da lumana a dukkan sassan kasar, Daily Trust ta ruwaito.
Shugaban kasar ya bada wannan tabbacin ne a ranar Talata yayin da ya ke taya iyalan 'yan sandan da aka rahoto 'yan ta'addan kungiyar 'yan aware a Kudu maso Gabas sun yi wa kisar gilla suka kuma dauki bidiyo suka baza a dandalin sada zumunta.
Ya ce, "nan ba da dadewa ba mutane za su dena zaman makoki ko jimami saboda rasa rayyuka a kasar."
Shugaban kasar, cikin sanarwar da ya fitar mai lakabin 'Shugaban Kasa Ya Mika Ta'ziyya ga Iyalan Yan Sandan Da aka Yi wa Kisar Gilla' ya ce yan sandan uku da aka sace, inda daga bisani aka kashe biyu, suna yi wa kasa hidima ne, kuma sana samar da tsaro da wadanda suka kashe su.
Shugaba Buhari, bayan aike wa da sakon ta'aziyya ga iyalan 'yan sandan, ya yi addu'ar Allah ya jikan wadanda suka rasu ya kuma bawa iyalansu hakurin rashi.
Daga karshe, Shugaban kasar ya mika ta'aziyya ga iyalan dukkan wadanda suka rasu a yankunan da ake fama da rashin tsaro a kasar, Daily Trust ta ruwaito.
Ya yi kira gare su da su rika tunawa cewa a haske ne ke yin nasara a kan duhu.
Buhari ga jami'an tsaro: Bana son sake jin motsin ƴan bindigan hanyar Kaduna zuwa Abuja
A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci shugabannin tsaron kasar nan da su kawo karshen ta’addancin da ke aukuwa a kasa musamman a hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ya sanar da hakan a ranar Alhamis bayan wani taro da shugaban kasa ya yi da kwamitin tsaron kasa, NSC a fadarsa da ke Abuja, Daily Trust ta ruwaito.
A cewarsa shugaban kasan ya ba ‘yan sanda da duk wasu jami’an tsaro ciki har da jami’an binciken sirri umarnin kada su zauna har sai sun kawo karshen ta’addanci, rashin tsaro, amsar kudaden fansa da sauransu a Najeriya.
Asali: Legit.ng