Katsina: Allah ya yi wa matar marigayi Sarki Kabir Usman rasuwa
- Allah ya yi wa matar marigayi Sarkin Katsina, Alhaji Kabir Usman Katsina, Hajiya Rakiya Kabir Usman, rasuwa
- Hajiya Rakiya ta rasu ta na da shekaru 82 a duniya kuma ta bar 'ya'ya takwas, daga ciki akwai tsohon jami'in hukumar Kwastam
- Ta rasu a ranar Lahadi inda aka sallaci gawarta tare da birne ta a cikin gidan sarautar Katsina a ranar Litinin da ta gabata
Katsina - Allah ya yi wa matar tsohon sarkin Katsina, Alhaji Kabir Usman Katsina, rasuwa. Hajiya Rakiyat Kabir Usman ta riga mu gidan gaskiya.
Ta na daya daga cikin matan aure da tsohon Sarkin Katsina, Alhaji Kabir Usman ya rasu ya bari a duniya, Daily Trust ta ruwaito.
Hajiya Rakiya ta rasu a daren Lahadi inda ta ke da shekaru 82 a duniya, Daily Trust ta ruwaito.
Mai magana da yawun masarautar Katsina, Mallam Ibrahim Bindawa, ya tabbatar da aukuwar wannan lamarin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An sallaci gawarta kamar yadda addinin Islama ya tanadar kuma an birne ta a ranar Litinin a cikin masarautar Katsina.
Daga cikin jiga-jigan da suka halarci jana'izar ta akwai ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, wakilin masarautar Daura, Alhaji Faruq Umar tare da wasu jami'an gwamnatin jihar Katsina.
Hajiya Rakiya Usman ta rasu ta bar 'ya'ya takwas, daga ciki akwai tsohon jami'in kwastam, Mallam Aminu Kabir.
Daga karshe: An nada sabon Sarkin Musawan Katsina
A wani labari na daban, labari da muke samu ya nuna cewa, Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman, ya yi na’am da nadin Sagir Abdullahi Inde a matsayin sabon Sarkin Musawan Katsina.
Kamar yadda jaridar Aminiya ta Daily Trust ta wallafa, hakan na kunshe cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Sallaman Katsina, wanda ya kuma kasance Sakataren Masarautar Katsina, Alhaji Bello Ifo.
“Muna sanar da al’umma daga yau Talata, 22 ga watan Satumban 2020, Sagir Abdullahi Inde ya zama Sarkin Musawan Katsina.
“Allah Ya taya shi riko Ya kuma ba shi ikon sauke nauyin da ya rataya a wuyansa,” in ji sanarwar.
Nadin nasa ya biyo bayan mutuwar tsohon Sarkin Musawan Katsina, Alhaji Muhammad Gidado Usman Liman.
Asali: Legit.ng