Daga karshe: An nada sabon Sarkin Musawan Katsina

Daga karshe: An nada sabon Sarkin Musawan Katsina

- Sarkin Katsina, Mai martaba Alhaji Abdulmumini Kabir Usman, ya aminceSagir Abdullahi Inde ya zama sabon Sarkin Musawan Katsina

- Sakataren masarautar Katsina, Alhaji Bello Ifo, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa

- Nadin nasa na zuwa ne bayan mutuwar tsohon Sarkin Musawan Katsina, Alhaji Muhammad Gidado Usman Liman, a ranar Laraba, 2 ga watan Satumban 2020

Labari da muke samu ya nuna cewa, Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman, ya yi na’am da nadin Sagir Abdullahi Inde a matsayin sabon Sarkin Musawan Katsina.

Kamar yadda jaridar Aminiya ta Daily Trust ta wallafa, hakan na kunshe cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Sallaman Katsina, wanda ya kuma kasance Sakataren Masarautar Katsina, Alhaji Bello Ifo.

KU KARANTA KUMA: Zaben Edo: Jam'iyyar NCP ta buƙaci a soke zaɓe, a hukunta Obaseki

Daga karshe: An nada sabon Sarkin Musawan Katsina
Daga karshe: An nada sabon Sarkin Musawan Katsina Hoto: @Daily_Nigerian/@aminiyatrust
Asali: Twitter

“Muna sanar da al’umma daga yau Talata, 22 ga watan Satumban 2020, Sagir Abdullahi Inde ya zama Sarkin Musawan Katsina.

“Allah Ya taya shi riko Ya kuma ba shi ikon sauke nauyin da ya rataya a wuyansa,” in ji sanarwar.

Nadin nasa ya biyo bayan mutuwar tsohon Sarkin Musawan Katsina, Alhaji Muhammad Gidado Usman Liman.

Idan za ku tuna, mun kawo maku cewa Allah ya yi wa Sarkin Musawan Katsina, hakimin Musawa, Alhaji Muhammad Gidado Usman Liman rasuwa, jaridar Daily Trust ta wallafa.

Marigayi Alhaji Muhammad Gidado Usman Liman ya rasu a ranar Laraba, 2 ga watan Satumban 2020 bayan gajeriyar rashin lafiya da yayi fama da ita.

Marigayin ya rasu yana da shekaru 77 a duniya kuma ya bar 'ya'ya biyu, Hajiya Binta da Hajia Maijidda, tare da jikoki da 'yan uwa da dama.

Daga cikin 'yan uwansa akwai fitaccen masanin tarihin nan, marigayi Yusuf Bala Usman da kuma dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Musawa da Matazu a tarayya, Ahmad Usman Liman.

Marigayi Muhammad Gidado Usman Liman, jika ne ga Sarki Muhammad Dikko, sarkin masarautar Sullubawa na farko a jihar Katsina.

KU KARANTA KUMA: Yunƙurin fatattakar Oshiomhole daga APC: Jigon PDP ya roƙi APC ta ɗaga mashi ƙafa

Hakazalika, marigayin shine hakimi na karshe da Sarki Usman Nagogo ya nada, kakan sarkin yanzu na Katsina.

Tuni aka birneshi kamar yadda addinin Islama ya tanadar a fadarsa da ke Sabon Gari, kwatas din karamar hukumar Musawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng