Tsohon Shugaban kasa Jonathan ya fadawa Shugabanni yadda za a samu zaman lafiya

Tsohon Shugaban kasa Jonathan ya fadawa Shugabanni yadda za a samu zaman lafiya

  • Tsohon shugaban kasa, Dr. Goodluck Jonathan sun ziyarci Sarkin kasar Opume, Amalate Turner
  • Goodluck Jonathan ya jagoranci wadanda suka yi karatu tare a 1981 zuwa wajen Mai martaban
  • Da yake jawabi, Jonathan ya bayyana muhimmancin ayi wa kowa adalci domin a zauna lafiya a kasa

Rivers - Tsohon shugaban kasa, Dr. Goodluck Jonathan ya yi kira ga shugabannin Najeriya da su rika la’akari da kowane bangare wajen tafiyar da mulkinsu.

Jaridar Vanguard tace Goodluck Jonathan ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya jagoranci tsofaffin daliban jami’arsa zuwa wajen Sarkin kasar Opume.

Jonathan da sauran ‘yan ajin shekarar 1981 a jami’ar Fatakwal sun ziyarci Mai martaba Amalate Turner a fadarsa da ke karamar hukumar Ogbia, jihar Bayelsa.

A cewar tsohon shugaban kasa, sai an tafi da kowa idan ana so a daina jin koke-koke da korafe-korafe da fafutukar da wasu suke yi na neman a barka Najeriya.

Kara karanta wannan

Rundunar soji ta kame jami'anta da suka ci zarafin wasu mazauna a yankin Abuja

Mu na da dinbin arziki a kasa - Jonathan

Hukumar dillacin labarai na kasa, NAN ta rahoto Dr. Jonathan yana cewa Ubangiji ya yi wa Najeriya arziki da ma’adanai da yawan al’ummar da za ta amfani kasar.

Tsohon Shugaban kasa
Dr. Goodluck Jonathan a Abuja Hoto: @Jonathangoodluck
Asali: Facebook

Jonathan yace ba za a ci moriyar arzikin ba, sai idan an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Da yake jawabi a gaban Sarki Amalate Turner, Dr. Jonathan ya bukaci shugabanni su dage wajen samar da kasar da ba a nuna bambancin kabilanci da sauransu.

“Idan shugabanni sun saki layi, babu tantama za a samu rashin hadin-kai da rashin jin dadi daga wadanda ke ganin ba a san daraja da kimarsu ba.” – Jonathan.

Har ila yau, rahoton yace tsohon shugaban kasar ya yi amfani da wannan dama wajen bayyana abubuwan da suke damun wannan jami’a ta UNIPORT da suka halarta.

Kara karanta wannan

2023: Saraki ya ziyarci wata jihar arewa kan kudirinsa na son hayewa kujerar Buhari

A na sa bangaren, Mai martaba Amalate Turner ya yi farin-cikin sake haduwa da wadannan Bayin Allah da suka yi karatu tare shekaru sama da arba’in da suka wuce.

Mutane su na zaune babu aiki

‘Yan Majalisar dattawa sun ce ba a daina daukar aiki ba domin har gobe ana bada aiki ta karkashin kasa, duk da ana karyar an sa takunkumi saboda karancin kudi.

An ji shugaban kwamitin daidaiton raba mukamai, Danjuma La’ah yana cewa akwai matasan da suka gama karatu shekaru 15 da suka wuce, har yanzu ba su samu aiki ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng