Hameed Ali ya hana jiragen sama 91 tashi a Najeriya saboda kin biyan kudin kwastam

Hameed Ali ya hana jiragen sama 91 tashi a Najeriya saboda kin biyan kudin kwastam

  • Gwamnatin tarayya ta ba hukumar kwastam umarni ta hana wasu jiragen sama har 91 barin kasa
  • An dauki wannan tsattsauran matakin ne saboda ba a biya kudi wajen shigo da jiragen saman ba
  • Hukumar kwastam ta ba hukumomin NCAA, FAAN da NAMA umarni ka da ta kyale jiragen su tashi

Abuja - Gwamnatin tarayya ta umarci hukumar kwastam ta tsare jiragen sama da wasu manyan attajiran Najeriya suka mallaka saboda kin biyan kudi.

Jaridar Punch ta ce kudin da gwamnati ta ke bin wadannan mutane ya haura Naira biliyan 30.

Bayan samun wannan umarnin daga fadar shugaban kasa, sai Kanal Hameed Ali (mai ritaya), ya aikawa hukumomin NCAA, FAAN da NAMA takarda.

Wannan takarda mai lamba number NCS/T&T/ACG/042/s.100/VOL.II da aka rubuta a ranar 2 ga watan Nuwamba, 2021, ta isa hannun shugaban NCAA.

Kara karanta wannan

Wani nau’in cutar COVID-19 mai mugun hadari da bai jin magani ya bulla a kasashen Afrika

Bayan Kyaftin Musa Nuhu, shugaban FAAN na kasa, Kyaftin Rabiu Yadudu da takwaransa na NAMA, Kyaftin Fola Akinkuotu, sun samu wannan takarda.

Takardar ta bukaci NCAA da NAMA da FAAN su tsare wadannan jirage, su hana su damar tashi. Kwastam ta dogara ne da wasu sassa na dokokin aikinta.

Jiragen sama
Jiragen sama a filin jirgi Hoto: nairametrics.com
Asali: UGC

Dogon binciken da aka dauka

Rahoton ya bayyana cewa hukumar kwastam ta fara bibiyar duk jiragen saman da aka shigo da su tun daga shekarar 2006 domin tabbatar da sun biya kudi.

Wannan bincike ya nunawa Hameed Ali cewa an shigo da jirage ba tare da an biya kwastam kudin da ya kamata ba, ta bukaci su biya bashinsu.

Masu wadannan jirage sun rubutawa shugaban kwastam takarda, su na korafi a kan wannan umarni.

Kara karanta wannan

N2.3tr muka ware don rabawa yan Najeriya kayan tallafin Korona, Gwamnatin tarayya

Jiragen da abin ya shafa

Wasu masu jiragen sun bayyana gaban kwamitin kwastam, sun kare kansu. Daga cikinsu akwai:

Dassault Falcon 7X, Falcon 900EX, Hawker 4000, Bombardier BD 700 1A10, Bombardier Global 5000, Bombardier Global 5500, Bombardier Challenger 605, Gulf Stream Aerospace, Bombardier BD 700, daBombardier Challenger 604.

Sai jiragen Embraer 505, Bombardier Global 6000, Embraer Legacy 600, Embraer Legacy 650, Bombardier INC CL 600-2B19, Challenger 601 3A-ER, Gulfstream G-IVSP, Gulfstream G450, Gulfstream G550, HS125-B50XP, EMB505 Phenom 300, Cirrus SR 20V, da Hawker 800XP

Motoci masu cin lantarki a Najeriya

A makon da ya gabata ne aka ji cewa Najeriya za ta shigo gari, bayan Zeetin Engineering ta bada sanarwar fara shirin kera motoci masu amfani da wutar lantarki.

Bayan motocin lantarki, kamfanin zai rika kera karafunan jiragen sama da na kasa da kayan gona.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng