Mun gano jarirai da suke karɓar albashi a Borno, Gwamna Zulum

Mun gano jarirai da suke karɓar albashi a Borno, Gwamna Zulum

  • Gwamnan Borno Farfesa Zulum ya ce an gano ma'aikatan bogi da ke karbar albashi a Shani ciki har da jarirai
  • Zulum ya ce a kowane wata ana asarar Naira biliyan 19 wurin biyan ma'aikatan na bogi a karamar hukumar Shani
  • Gwamnan ya ce an gano wani gida daya da akwai ma'aikatan bogi 300 yana mai cewa idan aka cigaba da haka nan gaba ba za a iya biyan albashi ba

Jihar Borno - Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya bayyana cewa an gano sunayen jarirai yayin aikin tantance ma'aikata da ake yi a karamar hukumar Shani ta jihar Borno.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an gano manyan ma'aikata ne ke karkatar da albashin da ake biyan ma'aikatan na bogi ciki har da jarirai.

Kara karanta wannan

'Kuncin rayuwa ta tunzura ni: Matashin da aka kama da hodar iblisa ta N2.7bn a filin jirgin Abuja

Zulum ya bayyana hakan ne a wurin bikin gargajiya ta Menwara a karamar hukumar Shani a ranar Asabar.

Mun gano jarirai da suke karɓar albashi a Borno, Gwamna Zulum
Gwamna Zulum ya ce an gano sunayen jarirai da ke karbar albashi a Borno. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Gwamnan ya ce:

"Bari in fada muku a karkashen aikin tantancewar, an gano sunayen jarirai yayin da ake biyan Naira miliyan 19 ga ma'aikatan bogi a karamar hukumar Shani a duk wata.
An gano cewa wani gida daya na da ma'aikatan bogi 300 kuma idan hakan ya cigaba, ina tsoron, karamar hukumar Shani ba za ta iya biyan albashin ma'aikatan ta ba a gaba."

Zulum ya yi taro da Sarkin Shani

Ya ce ya yi taro da Sarkin Shani, Alhaji Muhammadu Nasiru Mailafiya da wasu masu ruwa da tsaki game da lamarin kuma ya umurci kwamishinan kananan hukumomi da Masarautu, Sagum Mai Mele ya tantance aikin ya kuma mayar da ma'aikatan da aka kore su bisa kuskure.

Kara karanta wannan

Shugaban karamar hukuma a Kano ya fada hannun ICPC, ana zargin ya ci makudan kudi

Ya kuma ce wasu mutane yan damfara ne suka rika sayar da ayyukan da ya kamata yan asalin garin Shani su samu kan kudi N250,000, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnan Borno ya yiwa manoma rabon kayan aiki

Daga bisani gwamnan ya yi rabon kayan noma ga mutane 1,750 a kananan hukumomin Shani, Bayo da Hawul.

Ya ce kowanne manomi ya samu injin ban ruwa, buhun taki, karamin buhun irin shinkafa da masara tare da maganin kashe ciyayi da kwari.

Ya bukaci manoman su yi amfani da kayan da hanyar da suka dace yana mai cewa badi ma za a sake yi wa manoman rabon kayan noma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: