'Dan sanda ya gano matarsa na faɗa wa samarinta bata da aure, ya faɗa wa kotu shima ya haƙura da ita

'Dan sanda ya gano matarsa na faɗa wa samarinta bata da aure, ya faɗa wa kotu shima ya haƙura da ita

  • A ranar Alhamis wani dan sanda mai shekaru 45, Rafiu Ademola, ya kai korafi wata kotu yana bukatar a raba aurensu mai shekaru 14
  • Hakan ya biyo bayan zargin rashin kamun kai da yake yi wa matarsa inda ya bayyana yadda ya ga sakon maza a wayarta su na bukatar su hadu a wurare daban
  • A cewarsa har sanar da samari take yi cewa bata da aure, kuma tana da son jiki don ko girki ba ta yi masa sannan ba ta girmama iyayensa

A ranar Alhamis wani dan sanda mai shekaru 45, Mr Rafiu Ademola ya bukaci a raba aurensu mai shekaru 14 da matarsa bisa zarginta da rashin kamun kai, The Pulse ta ruwaito.

Ya fada wa kotu cewa ya ga sakonni a wayarta inda ta ke fada wa samari cewa ba ta da aure.

Kara karanta wannan

Martanin mutane kan wani saurayi da ya kori budurwa saboda ba tayi kama da hotunan Istagram ba

Matar ɗan sanda ta faɗa wa saurayin ta bata da aure, mijin ya faɗa wa kotu shima ya haƙura da ita
Matata ce wa samarinta ta ke yi bata da miji, Dan sanda ga kotu. Hoto: The Nation
Asali: Getty Images

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

“Na ga sakonni a WhatsApp dinta wanda take yi da abokan barikinta, wadanda take haduwa da su a wurare daban-daban.
“Ta kan sanar da mazan cewa ba ta da aure ta na zama da ‘yar uwarta ne.
“Na tura duk sakonnin cikin wayata don kafa shaida.”

Mutumin ya ce matarsa ta na da son jiki kuma ko girki bata yi masa, ya ce ko iyayensa ba ta girmamawa.

Ya ce ya daina son matarsa

Ya sanar da kotu cewa ya daina son matarsa, a taimaka a raba aurensu don ba zai iya ci gaba da ajiye ta a gidansa ba.

Sai dai a bangaren Rashidat ta musanta zargin da mijinta yake mata inda ta amince da batun raba auren.

Ta shaida cewa tana rike wa mijinta kanta kuma bata taba bin wani namiji ba da sunan lalata hasali ma mijin ne ya ke kai mata cikin gidansu.

Kara karanta wannan

Wata mata mai shekaru 40 da ta haifawa mijinta 'ya'ya 44 tace ya gudu ya barsu

Ta bayyana yadda bai dade da fatattakarta daga cikin gidansa ba inda ya mayar da wata karuwarsa gidan don yanzu haka a shagonta take kwana.

Rashidat ta ce har dukanta ya na yi

Telar mai shekaru 40 ta zargi mijinta da mayar da ita gangar tashe ta hanyar dukanta duk sanda ya ga dama.

A cewarta har tsirara ya taba korarta daga gidan kuma dama mahaifiyarsa ba ta son ta, a gaban mutane ta ke tozarta ta.

Rashidat ta bukaci kotu ta ba ta damar rike yaransu saboda rashin kulawar da ake yi musu.

Alkalin kotun, Mr Adeniyi Koledoye ya bukaci dukansu da kasancewa masu hakuri sannan ya dage sauraron karar zuwa ranar 16 ga watan Disamba.

Kano: Mata ta garzaya kotun shari'a ta nemi a raba aurenta da mijinta saboda murguɗa baki

A wani labarin, mata ta maka mijin ta gaban kotu don bukatar a raba auren su sakamakon yadda rikici da tashin hankali ke aukuwa tsakanin su.

Kara karanta wannan

Shi kaɗai ya san inda na ke ajiye asusun: Budurwa ta faɗa wa kotu saurayin ta ne ya sace mata kuɗi

Ta bayyana gaban Alkali Munzali Tanko na kotun musulunci da ke zama a Kofar Kudu a birnin Kano don gabatar da korafin ta bisa ruwayar Dala FM.

Kamar yadda ta ce, mijin na ta ya na ci wa iyayen ta mutunci kuma ba ya ganin darajar su ko kadan kamar yadda ya zo a ruwayar na Dala FM.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164