A cigaba da garkame Abdul-Jabbar, Kotun Shari'a ta sake hana beli Shehin Malami
- Tun watan Yuli, hukuma ta tsare shehim Malami, Sheikh AbdulJabbar Nasiru Kabara a jihar Kano
- Gwamnatin jihar Kano ta shigar da AbdulJabbar kotun Shari'a ne kan zargin kalaman batancin da basu dace ba
- Wannan ya biyo bayan mukabala da Gwamnatin jihar ta shirya tsakanin Malamin da sauran Malaman jihar Kano
Kano - Kotun Shari'ar Musulunci dake zamanta a Kofar Kudu a jihar Kano ta sake hana Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara beli bayan watanni da tsareshi, rahoton BBC Hausa.
Muhammad A Mika’il, wanda ke wakiltan Malam AbdulJabbar a kotu ya sake gabatar da bukatar gaban mai Shar'ia Ibrahim Sarki Yola a zaman kotun da aka yi ranar Alhamis, 25 ga Nuwamba, 2021.
BBC ta rahoto cewa Gwamnatin jihar Kano ta bi umurnin da kotu tayi na cewa a baiwa Malam AbdulJabbar kudi N20,000 don ya sayi litattafai kuma a kawo masa littafin Sahihul Bukhari da Sahihu Muslim.
Kotu tace za'a yi zama na gaba ranar 9 ga watan Disamba, 2021.
Na janye kalamaina: Abduljabbar ya amince malaman Kano sun yi nasara a kansa
Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya bayyana cewa, a yi masa afuwa kuma lallai ya janey maganganun da ya yi game Manzon Allah SAW wadanda ake ganin sun taba mutuncin ma'aiki.
A cikin wani sauti karo na biyu da ya aike wa sashen Hausa na BBC ranar Lahadi, malamin ya ce yana fatan "hakan ya zama silar gafara da rahama da jin kai gare ni".
Ya kara da cewa:
"Wadannan maganganu da suka fito daga bakina suka jawo ce-ce-ku-ce game da Ma'aiki SAW, na janye su na kuma janye su."
Wannan ya faru ne 'yan awanni bayan sautin farko da ya fitar a Lahadin yana neman afuwar wadanda suka fahimci cewa shi ne ya kirkiri kalaman batanci ga Annabi da ake zarginsa da yi.
Asali: Legit.ng