Shugaban karamar hukuma a Kano ya fada hannun ICPC, ana zargin ya ci makudan kudi
- Jami’an ICPC sun gurfanar da Alhaji Ibrahim Muhammad Abdullahi a gaban wani kotu a jihar Kano
- Hukumar ICPC tace shugaban karamar hukumar na Fagge ya karkatar da kudin haraji da aka biya
- Alkali ya bada belin ‘dan siyasar da aka fi sani da Shehi, za a cigaba da zama a farkon shekarar 2022
Kano - Hukumar ICPC mai yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ta gurfanar da shugaban karamar hukumar Fagge, bisa zargin karkatar da kudin jama’a.
Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Alhamis, 25 ga watan Nuwamba, 2021, cewa an kai karar Ibrahim Muhammad Abdullahi a wani babban kotun jiha.
Ibrahim Muhammad Abdullahi wanda aka fi sani da Shehi ya bayyana gaban kotun, inda ya bayyana cewa bai aikata laifuffukan da ake zarginsa da yi ba.
Lauyoyin ICPC na tuhumar Shehi da laifuffuka hudu da suka alakanci karkatar da 20% na kudin harajin da malaman harai suka tara a karamar hukumar Fagge.
Abin da doka tace a biya malaman haraji daga kason abin da aka tattara shi ne kashi uku zuwa hudu. Amma Shehi ya ware masu har kashi 20 cikin 100 na kudin.
Ta'adin da Ibrahim Muhammad Abdullahi ya yi
Hukumar ICPC ta bakin lauyoyinta, ta ce a 2018 Alhaji Ibrahim Muhammad Abdullahi ya ware N689, 000 ya biya ma’aikatan haraji da sunan ladan aikin da suka yi.
Bayan watanni uku sai shugaban karamar hukumar ta Fagge ya sake yin irin wannan laifi, ya biya wani jam’i mai suna Sani Ibrahim, N733, 000 daga harajin jama'a.
A wannan wata na Yunin 2018, Shehi ya sake daukan kudi har N338, 560, ya ba wani Malam Abdullahi Adamu. Lauyoyin na ICPC suka ce wannan ya saba doka.
Kafin nan, ana zargin Ibrahim Abdullahi da biyan Abdullahi Adamu N399, 999 wanda shi ne kashi 20 na cikin dari na harajin da aka samu a karamar hukumar ta Fagge.
Alkali ya daga zaman kotu sai shekara mai zuwa
Solacebase tace wadannan aika-aika da Ibrahim Muhammadu Abdullahi watau Shehi yake yi, sun sabawa sashe na 19 na dokar ICPC wanda aka kafa a shekarar 2000.
Alkali mai shari’a Jamilu Shehu Sulaiman yace tun da wanda ake tuhuma yana kan mulki ne, ya bada belin shi a kan N500, 000, ya kuma daga kara sai Junairun 2022.
Tsohon gwamna da SGG sun ci N1.5bn?
Hukumar EFCC ta shigar da kara a kotu inda ku ka ji ta na zargin Sanata Jonah Jang da hada kai da sakataren gwamnatin Filato da wani akawun, wajen satar kudi.
Wani shaida da aka gabatar a kotu yace Yusuf Gyang Pam ya taimaka wajen wawurar kudi daga asusun gwamnati a lokacin da Jonah Jang yake gwamna tun 2015.
Asali: Legit.ng