Yanzu-Yanzu: JAMB ta bankado ciwa-ciwar bada Admishin 706,189 a Jami'o'in Najeriya
- Hukumar JAMB ta bankado yadda manyan makarantun gaba da sakandire suka bada gurbin karatu 706,189 ba tare da bin doka ba
- Shugaban JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, yace laifin ya karade makarantu daga kowane yankin Najeriya 6 da ake da su
- Yace tuni ministan ilimi, Malam Adamu Adamu, ya bada umarnin matakin da za'a ɗauka
Abuja - Shugaban hukumar shirya jarabawan shiga manyan makarantun gaba da sakandire (JAMB), Farfesa Ishaq Oloyede, a ranar Talata, yace hukumar ta gano yadda akai ciwa-ciwan bada gurbin karatu 706,189.
The Nation ta rahoto shugaban JAMB ɗin ya bayyana cewa ciwa-ciwan bada gurbin karatun ya shafi jami'o'i, kwalejin Ilimi, kwalejin fasaha da sauransu.
Oloyede ya yi wannan furucin ne a wurin taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a Abuja, yace irin wannan bada admishin ba kan ka'ida ba ya bata martaban Najeriya.
Ya kara da da cewa wannan ciwa-ciwan ya shafi dukkan sassa 6 da Najeriya ta kunsa, kuma a manyan makarantun gaba da sakandire masu zaman kansu da na gwamnati.
Ya alkaluman bada gurbin ba kan doka ba yake?
Kimanin jami'o'i 114 ne suka bayar da gurbin karatu 67,795 ba kan doka ba, yayin da kwalejin 137 suka bada gurbi 489,918.
Sai kuma Kwalejin ilimi guda 80 da hukumar ta gano sun bada gurbin karatu 142,818 ba kan ka'ida ba, da kuma sauran makarantu 37 waɗan da ke da hannu a bada Admishin 5,678.
Bugu da kari shugaban JAMB yace baki ɗaya wannan laifin an aikata shi tsakanin 2017- 2020.
Dailytrust ta rahoto Oloyede yace:
"Daga cikin matakan da muka ɗauka don dakatar da irin haka, ministan Ilimi ya amince da hujjojin JAMB na baiwa waɗan da aka gano dama ta ƙarshe."
"Ya kuma amince duk makarantun da suka aikata laifin su bayyana adadin ɗaliban da suka baiwa gurbi ba kan ka'ida ba daga 2017-2020 ta hanyar rubuto wasikar amsa laifi ga shuagaban JAMB."
"Daliban da suka cancanta zamu amince da su domin kawo karshen lamarin. Daga nan kuma JAMB zata fara wayar da kan al'umma kan hatsarin karban irin wannan gurbin daga yanzu."
Oloyede ya tabbatar da cewa daga yanzu babu wata dama da jami'o'i zasu samu wajen yin ciwa-ciwan bada admishin ba kan ka'ida ba, da sauran makarantu.
A wani labarin na daban kuma Shugaba Buhari na jagorantar taron majalisar zartarwa FEC a Aso Villa
Hadimin shugaban, Buhari Sallau, shine ya bayyana haka a wani rubutu da ya fitar a dandalin sada zumunta tare da hotuna.
Majalisar zartarwan tarayyan Najeriya ta kunshi shugaban kasa, mataimakinsa, SGF, ministoci da sauran su.
Asali: Legit.ng