Kotu ta daure jami’in gwamnatin tarayya a dalilin lakume miliyoyin kudin kwangila
- Hukumar ICPC tace wannan karo tayi nasara a shari’ar da take yi da Dasel Nanjwan a kotu a Kalaba
- Alkali ya zartar da hukuncin daurin shekara uku ga Mista Dasel Nanjwan bayan an same shi da laifi
- Mai magana da yawun bakin ICPC yace an yanke wannan hukunci ne a kotun daukaka kara a Kalaba
Cross River - Wata kotun daukaka kara da ke zama a garin Kalaba, jihar Kuros Riba ta yankewa Dasel Nanjwan hukuncin dauri bayan samun shi da laifi.
Jaridar Premium Times tace wannan Mista Dasel Nanjwan yana aiki ne a hukumar NEPZA ta tarayya. An same shi ne da badakalar cin kudin kwangila.
Hukumar ICPC mai yaki da cin hanci da rashawa ta fitar da jawabi a makon nan, inda ta bayyana cewa kotun daukaka kara ta samu Nanjwan da rashin gaskiya.
ICPC tace babban kotun tayi fatali da hukuncin da aka yi a baya, wanda babban kotun tarayya da ke garin Kalaba ya wanke jami’in daga laifin da ake zarginsa.
Matsalar da jami'in ya samu
Nanjwan ya na cikin kwamitin gwamnatin tarayya da ke tattaunawa da kamfanin General Electric (GE) Africa domin jawowa Najeriya hannun jari daga waje.
Rigimar ita ce Nanjwan ne ya mallaki kamfanin Kwop-ri Services da ya samu kwangilar da gwamnati ta bada na miliyoi, wanda hakan ya saba doka.
An rusa hukuncin karamar kotu
Da hukumar ICPC ta kai shi kara gaban Alkali Emily Ibok bisa zargin rike wata riba da aka samu a kudin kwangila Naira miliyan 342, sai Alkalin ya wanke shi.
Ganin hukuncin da aka yanke a 2019 bai yi mata ba, hukumar ta daukaka kara zuwa kotu na gaba, wannan karo suka yi nasara aka yi watsi da wancan shari’a.
An gurfanar da shugaban ƙaramar hukuma kan karɓar cin hanci na miliyoyi daga hannun ɗan kwangila a Abuja
Mai magana da yawun bakin hukumar ICPC na kasa, Mista Azuka Ogugua ya shaidawa This Day cewa an yankewa Nanjwa daurin shekaru uku a gidan yari.
An zartar da wannan hukunci ne a ranar Litinin, 22 ga watan Nuwamba, 2021. Kawo yanzu ba mu ji ta bakin lauyoyin da suka tsayawa Dasel Nanjwan a kotu ba.
Kowa ya yi ta kansa a Najeriya
A jiya aka ji ma’aikatar kasar wajen Sin ta fadawa jama’anta cewa kowa ya yi ta kan sa saboda rashin tsaro da ake fuskanta a wasu yankunan da ke Afrika.
Sanarwar ta na zuwa ne bayan an yi garkuwa da wasu Sinawa a jihar Kogi da wani kauye a kasar Kongo. Gwamnatin Sin ta ja-kunnen 'yan kasarta su yi hattara.
Asali: Legit.ng