Farashin mai na iya tashi N340 ga Lita a sabon shekara, GMD na NNPC
- An yi taron Bankin Duniya ranar Talata kuma maganganu sun yawaita kan lamarin tallafin man fetur
- Masu ruwa da tsakin da suka halarci taron sun yi ittifakin cewa kawai a cire tallafin mai a 2022
- Shugaban kamfanin NNPC ya bayyanawa yan Najeriya farashin da mai ka iya a sabuwar shekara
Dirakta Manaja na kamfanin NNPC, Malam Mele Kyari, ya tofa nasa albarkacin bakin kan lamarin cire tallafin man fetur a sabuwar shekarar 2022 da ake fuskanta.
A nasa jawabin, ya bayyana sabon farashin man da ake sa rai na iya konawa tsakanin N320 da N340 ga lita, rahoton Vanguard.
A cewarsa, da tun shekarar 2020 za'a cire tallafin amma wasu matsaloli suka taso kuma aka fasa hakan.
Yace amma daga 2022, doka ta wajabtawa gwamnati cire tallafin gaba daya.
A cewarsa yanzu babu wani damar yin haka a doka, amma na san akwai wani aiki babba kan gwamnati na kula da talaka.
Kyari ya bada tabbacin cewa za'a cire tallafin a 2022 kuma farashin mai
Zamu kara kudin mai, amma zamu fara baiwa yan Najeriya N5,000 kudin mota a wata: FG
Mun kawo muku cewa Ministar kudi, kasafin kudi da shirye-shiryen kasa, Zainab Ahmad Shamsuna, ta bayyana cewa Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari zata cire tallafin man fetur a 2022.
Idan Gwamnati ta cire wannan tallafi, kudin man fetur zai yi tashin gwauron zabo.
A madadin wannan tashi, Ministar kudin ta bayyana cewa Gwamnati za ta fara rabawa talakawan Najeriya dubu biyar-biyar a wata matsayin kudin mota.
Zainab ta bayyana hakan ne ranar Talata a taron kaddamar da rahoton Bankin Duniya (NDU).
A cewarta, talakawan dake Najeriya mutum guda milyan 30 zuwa 40 za'a rika baiwa wannan kudi wata-wata.
Tace amma sai an cire tallafin za'a san adadin yan Najeriya da zasu samu wannan kudi.
Asali: Legit.ng