Da Dumi-Dumi: Jami'an hukumar EFCC sun damke tsohon minista Fani-Kayode

Da Dumi-Dumi: Jami'an hukumar EFCC sun damke tsohon minista Fani-Kayode

  • Hukumar EFCC ta kama tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani Kayode, bisa zargin magudin takardu
  • Rahotanni sun bayyana cewa yanzu haka jami'an hukumar EFCC sun kai Kayode Ofishin su dake jihar Legas a yau Talata
  • Kakakin EFCC, Wilson Uwujaren, ya tabbatar da faruwar lamarin, amma bai yi cikakken bayani kan zargin da ake masa ba

Lagos - Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya shiga hannun hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC) a jihar Legas.

Punch ta rahoto cewa tsohon ministan na karkashin binciken hukumar ne bisa zargin amfani da jabun takardu da kuma magudi.

Rahotanni sun bayyana cewa jami'an EFCC sun kai tsohon minista Kayode ofishinsu na jihar Legas ranar Talata.

Kara karanta wannan

EFCC na neman wasu 'yan Nigeria 4 ruwa a jallo, ta saki hotunansu

Fani-Kayode
Da Dumi-Dumi: Jami'an hukumar EFCC sun damke tsohon minista Fani-Kayode Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Femi Fani-Kayode, wanda aka fi sani da FFK a takaice, ya sake komawa jam'iyyar APC mai mulki a watan Satumba, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Kakakin hukumar EFCC, Wilson Uwujaren, ya tabbatar da cewa jami'ai sun taso keyar FFK, amma yaki yin karin haske kan zargin da ake masa.

Da aka tambaye shi kan labarin kame tsohon ministan, Uwujaren yace:

"Eh, ina tsammanin wani abu kamar haka ya faru," amma bai ƙara cikakken bayani kan zargin da ake masa ba.

Kayode ya jima yana fafatawa da EFCC

FFK ya jima suna takun saƙa da hukumar EFCC na tsawon lokaci, kuma ta taɓa tsare shi na tsawon kwanaki 67 a shekarar 2016, tare da tsohon ministan kudi, Nevada Usman.

EFFC ta tuhume su da sauran wasu mutum biyu bisa zargin aikata wasu manyan laifuka da suka hada da zamba da kuma karkatar da kuɗaɗen al'umma da suka kai kimanin biliyan N4.9bn.

Kara karanta wannan

EFCC ta sake gurfanar da dan uwan Saraki da tsohon kwamishinan Kwara

Sai dai baki ɗayan su, sun musanta zargin da ake musu, kuma daga baya kowanen su ya samu beli kan miliyan N250m.

A wani labarin na daban kuma Shekih Ahmad Gumi ya sake jagorantar tawagar Malamai da Likitoci zuwa wani daji a jihar Kogi

Rahotanni sun bayyana cewa Shehin malamin da yan tawagarsa sun je Rugan ne domin tallafawa Fulanin ta bangaren duba lafiya.

Shugaban rugar Fulanin, Ardo Zubairu, ya nuna jin daɗinsa da ziyarar malamin, tare da rokon a gina musu makaranta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262