Shekih Ahmad Gumi ya sake jagorantar tawagar Likitoci zuwa wani daji a jihar Kogi
- Sheikh Ahmad Gumi ya jagoranci tawagar malamai da kuma likitoci zuwa wata rugar Fulani a dajin dake jihar Kogi
- Rahotanni sun bayyana cewa Shehin malamin da yan tawagarsa sun je Rugan ne domin tallafawa Fulanin ta bangaren duba lafiya
- Shugaban rugar Fulanin, Ardo Zubairu, ya nuna jin daɗinsa da ziyarar malamin, tare da rokon a gina musu makaranta
Kogi - Shahararren malamin nan, Sheikh Ahmad Gumi, ya jagoranci tawagar malamai da likitoci zuwa Rugan Ardo Zubairu Okebukun dake yankin karamar hukumar Yagba a jihar Kogi.
Tribune Online ta rahoto cewa shehin malamin da tawagarsa sun je Rugan ne domin tallafawa fulanin dake rayuwa a wurin ta bangaren lafiya.
Da yake jawabi a wurin, kakakin masallacin Sultan Bello, Nasir Ayuba, wanda ya yi magana a madadin tawagar, ya roki Fulanin su nemi ilimin zamani da na Addini.
Hakanan kuma ya roki baki ɗaya Fulanin dake rayuwa a yankin da su guji sa kai a rikici kuma su yi fatali da shiga aikin ta'addancin yan bindiga.
Mun ji dadin zuwan ku - Ardo
Da yake musu barka da zuwa, shugaban Fulanin, Ardo Zubairu, ya yaba wa Dakta Gumi da yan tawagarsa bisa zuwan su da niyyar taimaka musu.
Ya bayyana cewa tuni Fulanin dake yankinsa suka rungumi harkan neman ilimi domin inganta rayuwarsu ta yau da kullum, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
A cewarsa da yawa daga cikin mazauna rugan sun mallaki shaidar kammala karatun digiri na farko, wasu ma harda na biyu.
Ya kara da cewa filin kiwon dabbobi na Ayangban, gwamnatin jiha ta ware shi ne saboda Fulani makiyaya kaɗai, yace:
"Muna jin daɗin yadda gwamnatin jihar Kogi ke tallafa mana, muna da kayan more rayuwa a wurin kamar fanfon tuka-tuka, wurin duba lafiya da sauransu."
Ardo Zubairu ya gode wa Sheikh Gumi da tawagarsa, kuma ya roke su da su taimaka a gina musu makaranta a wurin domin basu da ita.
Ya kamata gwamnati ta rungumi haka
A nasa jawabin Dan iyan Fika, Mamu Tukur, ya kara jaddada amfanin irin wannan ziyara ta zaman lafiya da haɗin kai a matsayin hanyar kawo karshen ayyukan yan bindiga.
Yace:
"Matukar gwamnati ta rungumi neman zaman lafiya ta irin haka, kuma ta haɗa kai da masu ruwa da tsaki, to duk waɗan nan matsalolin masu sauki ne."
A wani labarin na daban kuma Shugaban majalisar malamai na kungiyar Izala ya magantu kan tsarin mulkin karba-karba a 2023
Sheikh Sani Yahaya Jingir yace babu wanda ya isa ya siyar da kuri'un mutane da sunan karba-karba a 2023.
Shehin Malamin ya kira tsarin da wani abu mai kama da caca, kuma a cewarsa mutane kada su yarda da shi kwata-kwata.
Asali: Legit.ng