Babu wanda aka kashe a Lekki Toll Gate: Lai Mohammed ya yi watsi da rahoton kwamitin EndSARS

Babu wanda aka kashe a Lekki Toll Gate: Lai Mohammed ya yi watsi da rahoton kwamitin EndSARS

  • Akwai tufka da warwara cikin rahoton kwamitin da gwamnatin Legas ta baiwa aikin binciken Lekki Toll Gate, Lai Mohammed
  • Bayanan Ministan na zuwa kimanin mako guda bayan fitowar rahoton da akayi shekara guda ana tattarawa
  • Sau shida kenan Ministan Labaran Najeriya yana karyata kisan da aka yiwa yan Najeriya a Legas suna zanga-zanga

FCT Abuja - Ministan Labarai da al'adu, Lai Mohammed, a ranar Talata, ya jaddada cewa babu kisan kare dangin da ya faru a Lekki Toll Gate ranar 20 ga Oktoba, 2020.

Alhaji Lai ya bayyana hakan ne a hirarsa da manema labarai ranar Talata a Abuja inda yayi watsi da rahoton binciken kwamitin da gwamnatin Legas ta nada don binciken abinda ya faru.

A cewar Punch, Ministan yace duk tatsuniya ce.

Lai Mohammed ya yi watsi da rahoton kwamitin EndSARS
Babu wanda aka kashe a Lekki Toll Gate: Lai Mohammed ya yi watsi da rahoton kwamitin EndSARS Hoto: @NGRSenate
Asali: Twitter

Kara karanta wannan

Abun bakin ciki: Jam’iyyar PDP ta sake rashi na wani babban jigonta

EndSARS: Gwamnati ta yi karya, lallai an kashe dimbin matasa a Lekki Toll Gate, Kwamitin binciken jihar Legas

Kwamitin binciken da gwamnatin jihar Legas don tattaunawa da wadanda yan sandan SARS suka ci zarafinsu ta sakin rahoton bincikenta kan kashe matasan da akayi ranar 20 ga Oktoba, 2020.

Kwamitin ta kama jami'an Sojoji da yan sanda da laifin kisa da hallaka matasa masu zanga-zangar EndSARS a Lekki Toll Gate, jihar Legas ranar 20 ga Oktoba, 2020.

Kwamitin karkashin jagorancin Alkali, Dors Okuwobi, ta gabatar da rahotonta ga ofishin Gwamnan jihar Legas.

A ranar 20 ga Okroba, Jami'an Sojojin Najeriya sun bindige matasa masu zanga-zanga ba gaira, ba dalili a Lekki Toll Gate amma gwamnatin Najeriya bata daina karyatawa ba.

A rahoton mai shafuka 309, yan sanda da Sojoji ne suka hallaka wadannan matasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Tags: