Yanzu-Yanzu: Fitaccen jarumin Nollywood, Baba Suwe, ya mutu

Yanzu-Yanzu: Fitaccen jarumin Nollywood, Baba Suwe, ya mutu

  • Mr Babatunde Omidina, jarumin fina-finan Nollywood da Yarbanci ya rasu
  • Daya daga cikin 'ya'yansa Adesola Omidina ya tabbatar da rasuwar jarumin
  • Baba Suwe ya rasu yana da shekaru 67 a duniya bayan fama da rashin lafiya

Tsohon jarumin fina-finan Nollywood da Yarbanci, Babatunde Omidina da aka fi sani da Baba Suwe ya riga mu gidan gaskiya.

The Nation ta ruwaito cewa ya mutu ne a ranar Litinin yana da shekaru 67 a duniya.

Yanzu-Yanzu: Fitaccen jarumin Nollywood, Baba Suwe, ya mutu
Fitaccen jarumin Nollywood, Baba Suwe, ya mutu. Hoto: @twinsblog77
Asali: Instagram

Yarsa mai suna Adesola Omidina ce ta sanar da rasuwar baba Suwe.

Omidina ta ce, Jarumi, Baba Suwe, ya rasu a ranar 22 ga watan Nuwamba. Za a sanar da shirye-shiryen birne shi a nan gaba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Kada ka janye dokar hana shigo da shinkafar kasar waje, Gwamnan APC ga Buhari

Baba Suwe ya yi fice ne saboda barkwancinsa a fina-finan Nollywood da na Yarbawa.

Ya yi fama da rashin lafiya a shekarar 2018, hakan yasa yan Nigeria da dama suka taimaka masa da kudin magani ya tafi kasar waje ciki har da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo.

Takaitaccen tarihin Baba Suwe

An haife Baba Suwe ne a ranar 22 ga watan Agustan 1958 a Inabere Street, Lagos Island a karamar hukumar Ikorodu ta jihar Legas.

Ya yi kararun frimare a Jamaitul Islamial Primary School a Legas da Children Boarding School, Osogbo daga nan ya tafi Adekanbi Commercial High School a Mile 12, Legas.

Ya kuma samu takardan shaidan kammala karatun sakandare a Ifeoluwa Grammar School, Osogbo, babban birnin jihar Osun.

Ya fara fitowa a fina-finai ne a 1971 amma ya yi fice ne bayan ya fito a wani fim mai suna Omolasan wanda Obalende ya shirya.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Mai kula da sarrafa jiragen sama ya yanke jiki ya fadi, ya mutu ya na tsaka da aiki

Ya kara fice bayan ya fito a fim din Iru Esin, wanda Olaiya Igwe ya shirya a 1997.

Ya fito a fina-finai da dama a Nigeria kamar Baba Jaiye Jaiye, fim din da Funke Akindele da Femi Adebayo suka fito, dan tsohon jarumi Adebayo Salami.

A 2011, hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA, ta kama shi kan zargin safarar miyagun kwayoyi.

Allah ya yi wa ƙanin Aliko Dangote rasuwa

A baya, kun ji cewa Sani Dangote, mataimakin shugaban rukunin kamfanonin Dangote kuma kanin Alhaji Aliko Dangote ya riga mu gidan gaskiya.

Mista Dangote ya rasu ne a kasar Amurka a ranar Lahadi 14 g watan Nuwamban 2021 bayan fama da rashin lafiya kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Duk da bai kai dan uwansa kudi ba, Sani Dangote yana da hannun jari a bangarorin noma, banki, man fetur da sauransu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164