Da duminsa: Mai kula da sarrafa jiragen sama ya yanke jiki ya fadi, ya mutu ya na tsaka da aiki
1 - tsawon mintuna
- Aniekan Inuk Effiong ma'aikaci ne da ke kula da sarrafa jiragen sama a filin sauka da tashin jirage da ke jihar Legas
- Ma'aikacin ya yanke jiki ya fadi yayin da ya ke tsaka da aikinsa a sa'o'in farko na ranar Litinin, 22 ga watan Nuwamba
- Babu ko shurawa, Aniekan Inuk Effiong ya ce ga garinku inda ya rasu a take a yayin da ya ke bakin aikinsa
Legas - Aniekan Inuk Effiong mai kula da sarrafa jiragen sama ne da ke aiki da filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammed da ke Legas.
Kamar yadda Daily Trust ta tattaro, Aniekan Inuk Effiong ya yanke jiki ya fadi kuma a take ya sheka lahira a sa'o'in farko na ranar Litinin yayin da ya ke tsaka da aiki.
An gano cewa ya na tsaka da aiki ya yanke jiki ya fadi kuma babu dadewa ya sheka barzahu.
Karin bayani na nan tafe...
Asali: Legit.ng
Tags: