Taka dokar hanya: An kame baburan 'yan achaba a Legas, an murkeshesu a bainar jama'a

Taka dokar hanya: An kame baburan 'yan achaba a Legas, an murkeshesu a bainar jama'a

  • A kalla babura 482 da aka kama ne gwamnatin jihar Legas ta murkushe su a ranar Asabar, 20 ga watan Nuwamba
  • Rundunar ‘yan sandan jihar karkashin jagorancin Kwamishina Hakeem Odumosu ce ta jagoranci murkushe baburan
  • Odumosu ya ce an yi aikinne a bainar jama’a domin tabbatar wa ‘yan Legas cewa da gaske jihar ba za ta lamuncu karya dokokin hanya ba

Legas - Sakamakon karya dokokin hanya, sakateriyar Alausa da ke Ikeja, karkashin gwamnatin jihar Legas ta murkushe dimbin babura da aka kama a wurare daban-daban a Legas.

A watan Janairu, gwamnatin jihar ta haramta gudanar da ayyukan babura na kasuwanci - wanda aka fi sani da achaba - da babura masu kafa uku a kananan hukumomi 15, inji TheCable.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Gwamnati ta haramta siyar da babura a wata jihar arewa

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Hakeem Odumosu, ya halarci wurin da aka murkushe baburan akalla 482, inji rahoton The Sun.

Taka dokar hanya: An kame baburan 'yan achaba a Legas, an murkeshesu a bainar jama'a
Yadda aka murkshe babura sama da 400 a Legas | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Odumosu ya kara da cewa an yi aikin ne a bainar jama’a domin kawar da zagin da wasu ke yi na cewa ana sayar da baburan ne sannan a sake sarrafa su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanarwar da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Legas, CSP Adekunle Ajisebutu, ya fitar ta ce:

“Kwamishanan ‘yan sandan na fatan kara gargadin masu hawa babura da ke bin wuraren da aka kange da kuma masu karya dokar hanya ko amfani da babura wajen aikata miyagun laifuka a jihar da su canza shawara ko su fuskanci hukuncin shari’a.

“Kwamishinan ‘yan sandan ya ba da tabbacin cewa za a ci gaba da aikin murkushe baburan da suka taka doka, tare da nanata kudurin rundunar ‘yan sanda na tabbatar da doka.”

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi a jihar Nasarawa kan kisan wasu makiyaya

'Yan kasuwa a Legas sun yi zanga-zangar nuna adawa da 'yar shugaban APC Tinubu

A wani labarin, daruruwan ‘yan kasuwa ne a babbar kasuwar Oyingbo a ranar Laraba suka gudanar da zanga-zangar nuna adawa da Misis Folashade Tinubu-Ojo, diyar shugaban jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu.

Tinubu-Ojo ita ce Iya Oloja Janar na Najeriya, PM News ta ruwaito.

An ce ta rufe kasuwar ne mako guda da ya gabata, saboda matsalar muhalli yayin da ta kulle dukkan harkokin kasuwanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.