Duk ma'aikacin da bai yi rigakafin Korona ba nan da kwanaki 10 ba zai shiga Ofis ba
- Sakataren Gwamnatin Tarayya ya gargadi ma'aikatan gwamnatin da basu yi allurar rigakafi ba har yanzu
- Boos Mustapha yace ba za'a bari duk wanda bai yi rigakafi ba ko kuma yaki nuna hujjar bai da cutar Korona ba, ba shi ba shiga ofis
- Sauran kwanaki goma kacal zuwa ranar 1 ga Disamba da za'a fara dabbaka wannan doka
Abuja - Gwamnatin tarayya ta jaddada cewa duk ma'aikacin gwamnatin da bai yi rigakafin Korona nan da ranar 1 ga Disamba ba, ba zai samu damar shiga ofishinsa ba.
Sakataren Gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya bayyana hakan ranar Juma'a a Abuja yayin taron kamfen yiwa mutane rikakafin, rahoton DailyTrust.
Ya yi kira ga ma'aikatan gwamnati su ribaci kwanaki goma da suka rage cikin watan Nuwamba wajen yin rigakafin.
A cewarsa:
"Muna tunawa dukkan ma'aikatan gwamnatin tarayya cewa har yanzu mun kan bakanmu, ranar 1 ga Disamba, 2021 ne ranar karshe ga kowa ya nuna hujjar cewa yayi rigakafi ko kuma takardar sakamakon gwajin Korona na awanni 72 kafin a bari su shiga Ofis."
"Saboda haka ina kira ga ma'aikatan gwamnati da basu yi rigakafi ba su ribaci wannan dama don yi domin kare kawunansu da masoyonsu."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Adadin wadanda aka yiwa rigakafi kawo yanzu
Shugaban hukumar cigaban kananan asibitoci (NPHCDA), Dr Faisal Shuaib, ya bayyana adadin yan Najeriya da aka yiwa rigakafi kawo yanzu.
A cewarsa, kawo ranar 19 ga Nuwamba, yan Najeriya 5,989,480 suka yi allurar farko, yayinda mutum 3,341,094 suka yi alluran biyu gaba daya.
Asali: Legit.ng