Yanzu-Yanzu: Mayaƙan Boko Haram sun sha mummunan kaye hannun sojoji, mutane na can suna murna a Damboa
- Dakarun sojojin Nigeria da ke karamar hukumar Damboa a jihar Borno sun yi nasarar dakile wani hari a safiyar yau Juma'a
- Rahotanni sun bayyana cewa 'yan ta'addan sun shigo Damboa misalin karfe shida suna harbe-harbe
- Amma nan take dakarun sojojin da ke Damboa sun tari 'yan ta'addan suka fafata, sannan suka fatattake su daga yankin
Jihar Borno - Mutanen gari suna ta murna a karamar hukumar Damboa da ke jihar Borno bayan dakarun sojojin Nigeria sun yi nasarar fatattakar harin da 'yan ta'adda suka kawo a safiyar yau.
Sojojin sun tilasta wa mayakan Boko Haram ficewa daga kudancin jihar Borno, a cewar majiyoyi.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ƴan ta'addan sun afka garin Damboa ne misalin ƙarfe 6.35 na safe suka bude wuta.
Hakan ya tada hankalin mazauna garin amma dakarun sojoji suka tare su sannan suka fatattake su daga garin bayan musayar wuta.
Majiya daga rundunar sojoji ya shaidawa wakilin Daily Trust cewa yan ta'addan ba su cika minti 30 ba a garin bayan sojojin sun tare su.
Majiyar ta ce:
"Ina iya tabbatar maka cewa yan ta'adda sun yi yunkurin kai hari da safen nan amma ba su yi nasara ba, sojojin da ke Damboa sun fatattake su nan take."
Wani mamba na 'yan sa kai ya shaidawa majiyar Legit.ng Hausa cewa wasu mazauna garin sun samu rauni sakamakon harbin bindiga a Kala, wani gari da ke kusa da Damboa.
Majiyar ta ce:
"A kalla mutane 8 ne suka samu rauni sakamakon harbin bindiga a kauyen Kala kusa da Damboa."
"Dakarun sojojin sun yi bajinta a yanzu da muke magana ma mutane suna ta murna a Damboa."
Borno: Hotunan ragargazar da sojoji suka yi wa ISWAP a Askira Uba, sun kashe 50 sun kwato makamai
A wani labarin mai alaka da wannan, Rundunar Operation Hadin Kai ta Sojojin Nigeria da ke arewa maso gabas ta samu nasarar halaka mayakan ISWAP guda 50 a karamar hukumar Askira Uba.
Hedkwatar tsaron Najeriya ta shafin su na Facebook sun bayyana yadda sojojin su ka yi gaba da gaba da mayakan ISWAP wanda har lalata mu su kayan yakin su suka yi.
Lamarin ya auku ne a ranar Litinin, 15 ga watan Nuwamba inda jaruman sojin suka samu nasarar halaka manya da kananun mayakan kungiyar.
Asali: Legit.ng