Shugaban Najeriya Buhari zai ba Gwamnoni 36 bashin Naira Biliyan 650 da za a karba a 2051

Shugaban Najeriya Buhari zai ba Gwamnoni 36 bashin Naira Biliyan 650 da za a karba a 2051

  • Gwamnatin Tarayya za ta ba duka jihohin kasar nan 36 bashi da ruwan makudan kudi kwanan nan
  • A wajen taron NEC, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana wannan a Aso Villa
  • Jihohin za su biya wannan bashi nan da shekaru 30, sannan an kara masu ruwan 9% a kan uwar kudin

Abuja - Daily Trust ta rahoto cewa shugaba Muhammadu Buhari ya amince a rabawa gwamnoni Naira biliyan 656.112 domin su iya cike gibin da za su samu.

Mai girma mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana haka a lokacin da ya jagoranci taron majalisar tattalin arziki na NEC a birnin Abuja.

Da yake magana a ranar Alhamis, 18 ga watan Nuwamba, 2021, Yemi Osinbajo yake cewa za a bada wannan kudi ne domin jihohi su biya bashin da ke kansu.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya bi sahun Sheikh Gumi, Ya Bayyana hanyar da Buhari zai bi ya kawo karshen yan bindiga

Mai magana da yawun bakin mataimakin shugaban kasa, Laolu Akande, ya fitar da jawabi na musamman bayan taron NEC da aka yi a fadar shugaban kasa.

Jawabin na Laolu Akande ya nuna cewa za a dauki shekaru 30 kafin a kammala biyan wannan bashin. Haka zalika an sa wa gwamnonin jihohin ruwa na 9%.

Shugaban Najeriya
Shugaba Muhammadu Buhari a taron IATF Hoto: MuhammaduBuhari
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

CBN yana aiki a kan bada bashin

Ministar kudi, kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki, Zainab Ahmed, ta sanar da NEC cewa babban bankin kasa na CBN yana aiki a kan yadda za a ba jihohi bashin.

Rahoton ya bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta yi rabon wannan kudin ne a sahu shida, za kuma a dauki tsawon watanni shida kafin a kammala rabon biliyoyin.

A watan Yulin 2021 ne majalisar tattalin arzikin ta sanar da gwamnoni cewa za a fara cire wani kaso daga cikin kudinsu domin su biya bashin da suka karba a baya.

Kara karanta wannan

Yajin aikin ASUU: FG za ta rabawa jami’o’i biliyan N22.72 a ranar Laraba – Ministan Buhari

Daga nan ne jihohin suka nemi alfarma, suka roki gwamnatin tarayya ta ba su wadannan kudi.

Taron na NEC bai tashi ba sai da shugaban hukumar NPHCDA mai kula da cigaban dakunan asibitocin shan magani, Dr. Faisal Shuaib ya gabatar da rahotonsa.

Aikin hajjin shekarar nan

A ranar Talata ne aka ji Hukumar NAHCON tace hajjin shekarar 1443 zai sha ban-bam da sauran hajjin da ake yi a shekarun baya domin an shigo da fasahar zamani.

Wannan ne karon farko da za a sauke farali da kyau tun da annobar COVID-19 ta barke. NAHCON tace za a rabawa maniyyata wayoyi masu kunshe da wasu manhajoji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng