Saudi Arabiya ta kawo sababbin salo a shekarar 1443, mahajjata za su yi aikin hajji da wayoyi

Saudi Arabiya ta kawo sababbin salo a shekarar 1443, mahajjata za su yi aikin hajji da wayoyi

  • Wani jami’in NAHCOM ya bayyana yadda hajjin shekarar nan ya bambanta da sauran aikin hajjin baya
  • Prince Sheikh Momoh Sulaiman yace wannan karo hukuma za ta raba wayoyin zamani ga maniyyata
  • Akwai manhajoji a cikin wadannan wayoyin salula da dole sai da su za a iya shiga kasa mai tsarki a bana

Abuja - Akwai bambance-bambance da za a gani a aikin hajjin shekarar nan. Sheikh Momoh Sulaiman ya bayyana wannan a wata hira da Legit.ng Hausa.

Prince Sheikh Momoh Sulaiman wanda shi ne kwamishinan tsare-tsare, alkaluma, bincike da bayanai na hukumar aikin hajji ta kasa ya zanta da mu ta salula.

Kwamishinan na hukumar NAHCON ya bayyana cewa su na ta kokari domin ganin ba a bar Najeriya a baya ba a hajjin da za ayi a wannan shekara ta 1443.

Kara karanta wannan

Tabbas akwai aikin Hajji a shekarar 2022, Maniyayata su shirya, NAHCON

Za ayi amfani da na'urori wajen aikin hajji

“Wannan karo hajjin na zamani za ayi – kusan a kira shi E-Hajj. Duk abubuwan da na’urorin zamani ake yinsu. Za mu dage mu ga ba a bar mu a baya ba.”
“Akwai manhaja mai suna ‘Ikhtimarna’ da za ayi amfani da ita wajen zuwa kasa mai tsarki. Sannan akwai ‘Tawakalna', wanda da ita za ka iya shiga ko ina.”
“Idan babu wannan manhaja, ba za aka iya zuwa wurin cin abinci ko asibiti ba. Za ka sauke shi, kayi rajista, sai ka fara amfani da shi.” - Momoh Sulaiman.
Kwamishinan NAHCON
Jami'in NAHCON, Prince Sheikh Prince Mamoh Hoto: Sadiq Onyesansiye Musa
Asali: Facebook

Wadannan manhajoji da aka kirkira su na dauke da bayanan lafiyar mutum. Kafin mutum ya yi aiki da su, dole sai ya cika duk ka’idojin yaki da Coronavirus.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya ta amincewa kamfanonin wuta su kara kudin shan lantarki a 2021

Sai an yi wa mutum gwajin COVID-19 da alluran rigakafi kafin ya shiga Saudi. Idan aka samu mutum bai yi ba ko da takardun bogi, za a turke shi, ko ayi masa.

NAHCON za ta raba wayoyi, ta horas da alhazai

Jami’in na NAHCON yace duk wanda zai yi aikin hajjin bana sai ya san harkar yanar gizo. Don haka ne sashen ICT za su tashi-tsaye domin a ba maniyyata horo.

Prince Sheikh Momoh Sulaiman yake cewa NAHCON ta tanadi sashenta na ICT ya kara kokari domin kar a ji kunya wajen dawainiyar sauke farali a shekarar bana.

Bugu da kari, Momoh yace hukumar zata raba wayoyi dauke da wadannan manhajojin domin mafi yawan alhazan Najeriya ba su da ilmin zamanin da za a bukata.

Za ayi aikin hajji a bana?

Dazu ne aka ji cewa hukumar kula da aikin Hajji ta kasa, NAHCON ta bayyana cewa musulman Najeriya za su samu damar yin aikin Hajji a shekarar hijira ta 1443.

Kara karanta wannan

Rikicin VAT: Gwamnatin Buhari na tunanin sasantawa da Wike da Gwamnonin Kudu ta huta

Kwamishinan tsare-tsare, alkaluma, bincike da bayanai na hukumar NAHCON, Prince Sheikh Mamoh, yace akwai tabbacin maniyyata za su sauke farali a bana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng