Babu unguwar da babu yan kwaya a Najeriya, Janar Buba Marwa

Babu unguwar da babu yan kwaya a Najeriya, Janar Buba Marwa

  • Shugaban hukumar NDLEA ya kai ziyarar aiki jihar Plateau inda ya gana da shugabannin kananan hukumomi
  • A cewarsa, matsalar kwaya na daga cikin abubuwan dake rura wutar matsalar tsaron da muke fuskanta a Najeriya
  • Buba Marwa yace babu wata unguwa a Najeriya da babu yan kwaya

Jos, Plateau - Shugaban hukumar yaki da safara da ta'amuni da muggan kwayoyi NDLEA, Buba Marwa, ya ce babu unguwar da ta tsira daga matsalar yan kwaya a Najeriya.

Marwa ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da shugabannin kananan hukumomin jihar Plateau, rahoton TheCable.

Tsohon Sojan yace kimanin yan Najeriya milyan 15 ke ta'amuni da haramtattun kwayoyi.

A cewarsa, wannan abu na bada gudunmuwa wajen tsanantar matsalolin tsaron da kasar ke fama da su.

Kara karanta wannan

Yan Najeriya har sun gaji da kuka, kashe-kashen rayuka ya zama ruwan dare: Yakubu Dogara

Babu unguwar da babu yan kwaya a Najeriya, Janar Buba Marwa
Babu unguwar da babu yan kwaya a Najeriya, Janar Buba Marwa Hoto: NTA
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yace:

"Yanzu haka da nike magana, yan Najeriya milyan 15 ke ta'amuni da kwayoyi; kowani mutum daya cikin mutane bakwai na shan muggan kwayoyi."
"Babu unguwar da ta tsira a Najeriya daga kwaya, shiyasa muke fama da matsalolin tsaro ko ina."
"Shi yasa muke kira ga shugabannin kananan hukumomi su bamu hadin kai wajen kawar da matsalar kwaya a cikinmu."

Matasa sama da 172 sun haukace a jihar Zamfara

Aƙalla matasa 172 suka samu taɓin kwakwalwa saboda shan kwayoyi ba kan ƙa'ida ba cikin shekara 6 a jihar Zamfara.

Mataimakin kwamandan yaƙi da shan miyagun kwayoyi na hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA, reshen Zamfara, Ladan Hashim, shine ya bayyana haka ranar Alhamis.

Mista Ladan, yace hukumar NDLEA reshen jihar Zamfara ta kai matasa da dama asibitin mahaukata domin kula da su.

Kara karanta wannan

Gumi ya caccaki 'yan aware: Igboho da Kanu ne suka kunna wutar rikicin Fulani a kudu

Ladan ya yi wannan jawabi ne a wurin wani taro mai taken, 'Ɗalibai zasu kawo kyakkyawan canji a yaki da shan miyagun kwayoyi a makarantar kwalejin lafiya ta Zamfara.'

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng