Aljannar duniya: Hotunan cikin katafarun gidajen £45m na Ronaldo da motocin alfarma
- Cristiano Ronaldo, fitaccen dan wasan kwallon kafa, ya mallaki gidaje da motocin alfarma na gani da fadi wadanda suka kai darajar £45m
- Ya na da motoci kirar Bugatti guda uku wanda kowacce ta kai darajar £8.5, marsandi mai darajar £14,000 da kuma gidajen alfarma
- Dan kwallon kafan mai shekaru talatin da shida a duniya ya na da tabar dukiya da ta kai £363 miliyan a duniya yanzu haka
Fitaccen dan wasan kwallon kafa a duniya, Cristiano Ronaldo, mutum ne mai son shakawata da fantamawa a cikin dukiyarsa.
Kamar yadda UK Sun ta wallafa, Ronaldo ya na da gidaje da motoci masu darajar sama da £45 miliyan, daga katafaren gidan na Madeira mai darajar £7 miliyan zuwa motarsa kirar Bugatti mai darajar £8.5 miliyan har kan marsandin sa mai darajar £14,000.
Ronaldo na iya barin gidansa na Cheshire zuwa wadannan gidajen, uku kacal daga cikin katafarun gidajensu masu darajar sama da £23 miliyan.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ana bayyana cewa ya mallaki motoci kirar Bugatti tare da wata La Voiture Noire mai darajar £8.5 wacce guda goma kacal aka kera.
A wani rahoto, wallafar ta ce kusan dukkan dukiyarsa za a iya cewa ta na tattare da motocin alfarma sama da ashirin, gidajensa da ababen hawan da basu wuce daukar fasinja daya.
Tsohon zakaran kungiyoyin kwallon kafa na Real Madrid da Juventus mai shekaru talatin da shida ya na da dukiyar da ta kai £363 miliyan.
A dukkan aikinsa tun farko, ya samu, kashe tare da zuba hannayen jari na £789 miliyan, UK Sun ta wallafa.
Asali: Legit.ng