Basarake ya gwangwaje diyarsa da kyautar mota bayan ta kammala digiri da daraja ta farko

Basarake ya gwangwaje diyarsa da kyautar mota bayan ta kammala digiri da daraja ta farko

  • Basaraken Oyo, Oba Lamidi Adeyemi III, ya nuna farin cikinsa da ni'imar da Allah ya yi wa diyarsa a karatunta
  • Diyar Sarkin, Gimbiya Zainab Adebunmi Adeyemi, ta kammala karatun digiri da sakamako mafi girma, ta samu kyautar mota
  • Hotunan motar da suka watsu a kafafen sada zumunta ya jawo cece-kuce daga bakin mutane

Oyo - Basaraken Oyo wanda ake kira da Alaafin, ya nuna matukar farin cikinsa da murna yayin da ɗiyarsa, Gimbiya Zainab Adebunmi Adeyemi, ta kammala karatun digiri da sakamako mai daraja ta farko.

Goldmynetv ta rahoto cewa ta kammala karatunta da kyakkyawan sakamako daraja ta farko a kwas ɗin Physiology daga jami'ar Lead a Ibadan, jihar Oyo, ranar Lahadi 14 ga watan Nuwamba.

Yayin farin ciki da murnan wannan nasara, mahifinta, Alaafin of Oyo, Oba Lamidi Adeyemi III, ya bata kyautar sabuwar mota.

Kara karanta wannan

Manyan gobe: Hazikan matasa 'yan Najeriya 3 da suka kera motocin a zo a gani da kansu

Alaafin of Oyo
Basarake ya gwangwaje diyarsa da kyautar sabuwa mota bayan ta samu 'First Class,' Hotuna ya jawo cece kuce Hoto: goldmynetv
Asali: Instagram

A hotunan da suka watsu a kafafen sada zumunta, an hangi gimbiya na murmurshi yayin da take mika sakamakonta ga mahaifinta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kazalika Legit.ng Hausa ta samu wasu hotunan ta a kan sabuwar motarta sanye da kayan kammala karatu, ta zauna a saman motar cikin farin ciki.

Yan Najeriya sun tofa albarkacin bakin su

@______hrh_ thought yace:

"Ina taya ki murna, amma ku ɗan dakata, ba wannan motar bace ake haya 'TAXI' da ita a Abuja?"

@Babaceekay yace:

"Muna taya ki murna, amma wannan mota ba sabuwa bace, Tokunbo ce ajin farko."

@elenujabala thought yace:

"Wannan basaraken da kuka gani zai sami abubuwa da dama a cikin yayansa; masu hazaka, masu kuɗi, Fasto, Babalawo, gimbiya, yarima, yan fashi, masu garkuwa, sojoji, likitoci da sauransu."

@dot_man_dotun121 yace:

"Akwai dubbannin waɗan da suka kammala karatu da daraja ta farko, me kuka ba su kyauta? yayi kyau, Najeriya ba ta rago bace, wata rana sai labari."

Kara karanta wannan

Batun Jaruma Rahama Sadau da wasu sabbin muhimman abubuwa 4 da suka faru a Kannywood

@uncleobinna1 yace:

'"Bata bari arzikin mahaifinta ya ɗaɗa ta da ƙasa ba, yarinya mai tunani, Allah ya kawo miki nasarori a gaba."

A wani labarin kuma Wani Dalibin jami'a ya lakadawa lakcara mace dukan kawo wuka daga neman taimako

Wani ɗalibin dake 400- Level a jami'ar Ilorin (UNILORIN) ya lakaɗawa malamarsa a jami'a dukan kawo wuka.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne ranar Alhamis, lokacin da ɗalibin ya je ofishin malamar neman ta taimaka masa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262