EndSARS: Gwamnati ta yi karya, lallai an kashe dimbin matasa a Lekki Toll Gate, Kwamitin binciken jihar Legas

EndSARS: Gwamnati ta yi karya, lallai an kashe dimbin matasa a Lekki Toll Gate, Kwamitin binciken jihar Legas

  • Bayan shekaru daya da fara aiki, Kwamitin bincike ta kammala aikin da aka gabata a jihar Legas
  • Mambobin kwamitin tara sun gabatar da takardar binciken ga Gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu
  • Kafin a ankara, kwafin rahoton ya samu fita kuma yan Najeriya sun gani

Kwamitin binciken da gwamnatin jihar Legas don tattaunawa da wadanda yan sandan SARS suka ci zarafinsu ta sakin rahoton bincikenta kan kashe matasan da akayi ranar 20 ga Oktoba, 2020.

Kwamitin ta kama jami'an Sojoji da yan sanda da laifin kisa da hallaka matasa masu zanga-zangar EndSARS a Lekki Toll Gate, jihar Legas ranar 20 ga Oktoba, 2020.

Kwamitin karkashin jagorancin Alkali, Dors Okuwobi, ta gabatar da rahotonta ga ofishin Gwamnan jihar Legas.

A ranar 20 ga Okroba, Jami'an Sojojin Najeriya sun bindige matasa masu zanga-zanga ba gaira, ba dalili a Lekki Toll Gate amma gwamnatin Najeriya bata daina karyatawa ba.

Kara karanta wannan

An yi jana’izar Jigon jam’iyyar APC da yan bindiga suka kashe a hanyar Kaduna/Abuja

EndSARS: Gwamnati ta yi karya, lallai an kashe dimbin matasa a Lekki Toll Gate, Kwamitin binciken jihar Legas
EndSARS: Gwamnati ta yi karya, lallai an kashe dimbin matasa a Lekki Toll Gate, Kwamitin binciken jihar Legas
Asali: Getty Images

A rahoton mai shafuka 309, yan sanda da Sojoji ne suka hallaka wadannan matasa.

Wani sashen rahoton yace:

"Kisan gilla, zalunci da cin zarafin masu zanga-zanga dake zaune a kasa rike da tutar Najeriya, suna waken taken Najeriya, wannan kisan kare dangi ne."
"Lallai gwamnatin jihar Legas ta bakin gwamnan jihar ta gayyaci Sojoji wajen kuma an tura su Lekki Toll Gate a ranar 20 ga Oktoba, 2020."
"Kwamitin ta gano cewa an yi yunkurin rufa-rufa kan abinda ya faru ranar 20 ga Oktoba ta hana share Lekki Toll Gate kafin bincike."

Sau biyar kenan Ministan Labaran Najeriya yana karyata kisan

Ministan Labarai da al'adu, Lai Mohammed, a ranar Talata, ya jaddada cewa babu kisan kare dangin da ya faru a Lekki Toll Gate ranar 20 ga Oktoba, 2020.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi a jihar Nasarawa kan kisan wasu makiyaya

Sau biyar yana fadin haka a jawabansa tun bayan aukuwan lamarin.

Sakamakon haka aka kafa kwamitoci a jihar Legas domin binciken wadanda yan sanda suka zalunta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng