Gawar Sani Dangote za ta iso Kano daga Amurka a yau Talata domin jana'iza
- A yau Talata ne ake sa ran gawar Alhaji Sani Dangote za ta iso daga kasar Amurka inda ya rasu a ranar Lahadi bayan gajeriyar rashin lafiya
- Sani ya rasu ya bar tsohuwar mahaifiyarsa, Hajiya Mariya, matarsa daya, 'ya'ya takwas da kuma 'yan uwa mata da maza
- Duk da tuni masu makoki suka cika gidansu da ke kwatas din Koki a Kano, ana sa ran yin jana'izarsa a gidan Aliko Dangote da ke Nasarawa GRA
A yau Talata ake sa ran gawar Sani Dangote, kanin mashahurin mai arzikin Afrika, Alhaji Aliko Dangote, za ta iso Najeriya daga kasar Amurka inda ya rasu.
Daily Trust ta ruwaito cewa, Sani shi ne mataimakin shugaban kamfanonin Dangote kuma ya rasu a ranar Lahadi a Amurka bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.
Wata majiya makusanciya ga iyalan ta ce, "Sani Dangote tuni dama ya ke fama da sankarar hanji kuma ya tafi Amurka domin samun magani, amma kamar yadda Allah ya so, ya rasu ya na da shekaru 61.
"Babu shakka, iyalan Dangote sun matukar jin mutuwar nan, amma mun karba wannan rashin tare da fawwalawa Allah mai girma lamurranmu."
Sani ya rasu ya bar tsohuwar mahaifiyarsa, mata, 'ya'ya takwas da 'yan uwa mata da maza.
Tun bayan da labarin mutuwar Sani ta iso, masu ta'aziyya sun dinga kai kawo a gidan Dangote da ke Kwatas din Koki a birnin Kano.
Amma kuma Daily Trust ta ruwaito cewa,, akwai yuwuwar a yi sallar jana'izarsa a gidan Aliko Dangote da ke GRA Nasarawa.
A yayin da Daily Trust ta ziyarci gidansu da ke Kwatas din Koki, an ga yadda ake ta ciyar da jama'a kafin a kawo gawar mamacin.
"Mun tattaru ne a nan kamar yadda aka saba, kuma ba don masu aikin Hajiya Mariya ba, ba za mu san cewa Hajiya ta yi rashin daya daga cikin 'ya'yanta ba.
“Mun yi masa addu'a ta musamman kuma za mu cigaba da yi masa addu'ar samun rahamar Allah," Wata dattijuwar mata mai suna Malama Hinde Bako tace.
Dan uwan Hamshakin Attajiri a nahiyar Afirka, Aliko Dangote, ya rigamu gidan gaskiya
A wani labari na daban, mataimakin shugaban kamfanin Dangode Group kuma ɗan uwa ga Attajirin Afirka, Aliko Dangote, Sani Dangote, ya riga mu gidan gaskiya.
Rahotanni sun bayyana cewa Sani Dangote ya rasa rayuwarsa ne bayan fama da jinya a kasar Amurka ranar Lahadi.
Wannan na kunshe ne a wani gajeren sako da rukunin kamfanonin Dangote, Dangote Industries, suka buga a shafinsu na Facebook.
Asali: Legit.ng