Kaduna: Alƙalin kotun shari'a ya ƙwace wa Ibrahim awarwaron da buduwarsa ta bashi don soyayya

Kaduna: Alƙalin kotun shari'a ya ƙwace wa Ibrahim awarwaron da buduwarsa ta bashi don soyayya

  • A ranar Litinin, kotun musulunci da ke zama a Magajin Gari da ke jihar Kaduna ta umarci kwace awarwaro daga hannun wani matashi, Ibrahim inda ta ce hakan shigar banza ce
  • Bayan alkalin kotun, Murtala Nasir ya tambayi Ibrahim dalilinsa na sa awarwaron mata a hannunsa, ya bayyana a kotu cewa wata kawarsa ta ba shi kyauta
  • Daga nan alkalin ya umarci a kwace awarwaron kuma ya yi barazanar daure shi matsawar ya sake bayyana da shigar banza nan gaba

Jihar Kaduna - Wata kotun shari’ar musulunci da ke zama a Magajin Gari ta kwace awarwaron da ke hannun Aliyu Ibrahim bayan ya kai kara kotun.

NAN ta ruwaito yadda Ibrahim, wani matashi mai karancin shekaru ya bayyana gaban kotu sanye da awarwaron mata a hannunsa.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: An bindige mutane biyar yayin da jihar Imo ta sake daukar zafi

Kaduna: Alƙalin kotun shari'a ya ƙwace wa Ibrahim awarwaron da buduwarsa ta bashi don soyayya
Alƙalin kotun shari'a ya ƙwace wa Ibrahim awarwaron da buduwarsa ta bashi don soyayya. Hoto: Daily Nigerian
Asali: Facebook

Bayan Alkalin kotun, Murtala Nasir ya bukaci sanin dalilinsa na shigar banza, Ibrahim ya bayyana cewa kawarsa ce ta ba shi kyautar awarwaron.

Daga nan alkalin ya bukaci a amshe kuma ya yi barazanar daure shi matsawar ya sake irin wannan shigar a gaban kotu.

Daga baya Alkalin ya saki wandanda aka kai kara gaban kotun bisa zargin su da cin zarafi.

Dama dan sanda mai gabatar da kara, Luka Sadau ya ce a ranar 4 ga watan Satumba Ibrahim ya kai karar Anas da Aliyu Ussaini gaban ofishin ‘yan sanda da ke Magajin Gari.

Ibrahim ya ce har targade suka yi masa

Ya ce sun yi wa Ibrahim duka kamar bakon kare inda har tagada masa kafarsa ta dama sai da su ka yi.

Kara karanta wannan

Kungiyar PDP ta nemi Gwamna Wike ya nemi takarar kujerar shugaba Buhari a 2023

Ya sanar da kotu cewa laifin ya ci karo da sashi na 210 na Sharia Penal Code na jihar Kaduna a shekarar 2002.

Kano: Mata ta garzaya kotun shari'a ta nemi a raba aurenta da mijinta saboda murguɗa baki

A wani labarin, mata ta maka mijin ta gaban kotu don bukatar a raba auren su sakamakon yadda rikici da tashin hankali ke aukuwa tsakanin su.

Ta bayyana gaban Alkali Munzali Tanko na kotun musulunci da ke zama a Kofar Kudu a birnin Kano don gabatar da korafin ta bisa ruwayar Dala FM.

Kamar yadda ta ce, mijin na ta ya na ci wa iyayen ta mutunci kuma ba ya ganin darajar su ko kadan kamar yadda ya zo a ruwayar na Dala FM.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: