Kano ta yi cikar kwari yayin da mataimakin gwamna ya aurar da ‘yarsa

Kano ta yi cikar kwari yayin da mataimakin gwamna ya aurar da ‘yarsa

  • Jihar Kano ta zamo ba masaka tsinke a ranar Asabar, 13 ga watan Nuwamba, yayin da mataimakin gwamna, Nasiru Yusuf Gawuna, ya aurar da diyarsa
  • An kulla aure tsakanin Ahmad Abdul-One Muhammad da amaryarsa Fatima Nasir Gawuna kan sadaki N300,000
  • Taron ya samu halartan manyan mutane ciki harda Gwamna Abdullahi Ganduje da Mallam Ibrahim Shekarau

Kano - Jihar Kano ta yi cikar kwari a ranar Asabar, 13 ga watan Nuwamba, yayin da mataimakin gwamna, Nasiru Yusuf Gawuna, ya aurar da diyarsa.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa diyar mataimakin gwamnan ta auri masoyinta, dan marigayi manjo janar Abdul-One Muhammad.

Kano ta yi cikar kwari yayin da mataimakin gwamna ya aurar da ‘yarsa
Kano ta yi cikar kwari yayin da mataimakin gwamna ya aurar da ‘yarsa Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

An daura auren ango Ahmad Abdul-One Muhammad da amaryarsa Fatima Nasir Gawuna kan sadaki N300,000 wanda wakilin ango, Ambasada Dan-Kano ya gabatar.

Kara karanta wannan

Hotuna da sunayen jaruman Sojojin da aka kashe a artabu da yan ta'adan ISWAP

Taron wanda aka gudanar a Alu Avenue, karamar hukumar Nassarawa ta jihar, ya hada Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Malam Ibrahim Shekarau, sanata mai wakiltan Kano ta tsakiya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoton ya nuna cewa wannan shine karo na farko da shugabannin suka hadu tun bayan barkewar rikicin cikin gida a jam'iyyar All Progressives Congress (APC) reshen Kano.

Tuni Shekarau da sanata mai wakiltan Kano ta arewa, Barau Jibril da wasu yan majalisar wakilai hudu daga jihar suka kafa wata kungiya a APC, wanda Haruna Danzago ke jagoranta.

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai tsohon shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Adamu Mu'azu, tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Alhaji Yayale Ahmed, da ministan tsaro, Manjo Janar Aliyu Magashi (mai ritaya).

Sauran sun hada da Gwamna Mohammad Abubakar Badaru, tsohon gwamnonin jihohin Zamfara da Sokoto, Abdulazeez Yari da Aliyu Wamakko, sarakunan gargajiya da sauran manyan mutane.

Kara karanta wannan

Sunan Birgediya Janar da ya aka kashe harin kwantan baunan da ISWAP ta kai Borno yau ya bayyana

Sabuwa fil a leda nake, ban taba sanin ‘da namiji ba har nayi aure – Amarya mai shekaru 55

A gefe guda, masu iya magana kan ce da aure da mutuwa duk lokaci ne, hakan ne ya kasance ga wata 'yar Najeriya da ta kusa cire tsammani, domin sai da ta kai shekaru 55 kafin Allah ya bata mijin aure.

Allah ya kulla aure tsakanin matar mai suna Esther Bamiloye da angonta Isaac Bakare mai shekaru 62 wanda shima wannan ne aurensa na farko.

A wata hira da tayi da jaridar Punch, Esther ta bayyana cewar duk da dadewar da tayi ba tare da aure ba, ta yi kokarin ganin ta kare mutuncinta, domin a cewarta bata taba sanin 'da namiji ba kafin aurenta. Ta ce ita budurwa ce sabuwa fil a leda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng