Hukumar Sojin Najeriya ta tabbatar da kisan Birgediya Janar a harin kwantan baunar ISWAP
- Dakarun rundunar HADIN KAI sun hallaka yan ta'addan ISWAP a artabun da sukayi ranar Asabar
- Yayinda rundunar Birgediya Janar Dzarma Zirkushi taje kai dauki kuma, aka bude mata wuta
- Shugaban Hafsan Soji ya aika sakon ta'aziyyarsa ga iyalan babban Sojan da sauran da suka rasa rayukansu
Hukumar Sojin Najeriya tabbatar da kisan Birgediya Janar Dzarma Zirkushu, Kwamandan rundunar 28 Task Force Brigade, dake Chibok, jihar Borno, Arewa maso gabas.
Yan ta'addan sun kashe Janar din tare da wasu jami'ansa uku, yayinda suke hanyar =su ta zzuwa kai dauk ga Sojoji a kauye Bungulwa dake kusa Askira Uba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kakakin hukumar Sojin Najeriya, Onyeama Nwachukwu, ya sanar da hakan a jawabin da ya saki ranar Asabar, rahoton DailyNigerian.
Ya bayyana cewa:
"Dakarun rundunar HADIN KAI sun hallaka yan ta'addan ISWAP a artabun da sukayi a karamar hukumar Askira Uba a jihar."
"Abin takaici, babban jami'in Soja Birgediya Janar Dzarma Zirkusu da sojoji uku sun rasa rayukansu bayan taka rawar gani lokacin da suka kai dauki."
"Mun tuntubi iyalan babban Sojan da sauran sojojin."
An yi artabu tsakanin Soji da yan ta'addan ISWAP
Mun kawo muku cewa 'Yan ta'addan ISWAP sun yi musayar wuta da sojoji a wani sansanin soja da ke karamar hukumar Askira/Uba a jihar Borno.
Wasu mazauna sun ce sun hango mayakan na ISWAP a cikin wani dogon ayarin motocin bindigu a hanyar Ngude zuwa Askira, da sanyin safiyar yau.
Adamu Saleh ya shaida wa The Sun cewa:
“Al’amarin ya yi muni amma ‘yan ta’addan sun janye a yanzu.”
Mazauna sun yi ikirarin cewa sun kai rahoton zirga-zirgar 'yan ta'addan ga jami'an tsaro amma ba a dauki wani mataki ba kafin wannan mummunar kungiyar ta afkawa garin Askira bayan sa'o'i.
Asali: Legit.ng