Da duminsa: Daga Faransa, Shugaba Buhari ya garzaya kasar Afrika ta Kudu don halartan kasuwar baja koli

Da duminsa: Daga Faransa, Shugaba Buhari ya garzaya kasar Afrika ta Kudu don halartan kasuwar baja koli

Shugaba Muhammadu Buhari daga kasar Faransa zai garzaya kasar Afrika ta kudu don halartan kasuwar bajakolin Afrika fa za’a yi a birnin Durban.

Buhari zai tafi ranar Asabar, 13 ga watan Nuwamba, 2021.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Asabar.

Buhari zai samu rakiyar Ministan harkokin waje , Geoffrey Onyeama; Ministan kasuwanci da hannun jari, Otunba Niyi Adebayo; dss.

A cewar Adesina, Buhari zai dawo ranar Talata, 16 ga Nuwamba, 2021.

Da duminsa: Daga Faransa, Shugaba Buhari ya garzaya kasar Afrika ta Kudu don halartan kasuwar baja koli
Da duminsa: Daga Faransa, Shugaba Buhari ya garzaya kasar Afrika ta Kudu don halartan kasuwar baja koli
Asali: Facebook

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng