EFCC ta sake taso keyar tsohon Gwamnan da ya taba shiga kurkuku, ya fito saboda cin kudi

EFCC ta sake taso keyar tsohon Gwamnan da ya taba shiga kurkuku, ya fito saboda cin kudi

  • An tsare Lucky Nosakhare Igbinedion a hedikwatar hukumar EFCC domin ya amsa wasu tambayoyi
  • Lucky Nosakhare Igbinedion ya yi gwamna a jihar Edo tsakanin 1999 da 2007 a karkashin jam’iyyar PDP
  • Mai magana a madadin hukumar EFCC, Wilson Uwujaren ya tabbatar da cewa sun tsare tsohon gwamnan

Abuja - Tsohon gwamnan jihar Edo, Lucky Nosakhare Igbinedion, ya fada hannun jami’an hukumar EFCC, ana zarginsa da laifin satar kudin a’umma.

Jaridar Vanguard tace hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa sun tsare Cif Lucky Nosakhare Igbinedion a hedikwatarsu.

Lucky Igbinedion ya isa babban ofishin na EFCC da ke unguwar Jabi a garin Abuja da kimanin karfe 2:00 na ranar Alhamis, 11 ga watan Nuwamba, 2021.

Premium Times tace ana tuhumar tsohon gwamnan da wawurar Naira biliyan 1.6 daga baitul-mali.

Kara karanta wannan

Abubuwa 6 da suka ba Farfesa Soludo da APGA gudumuwa a zaben Gwamnan Anambra

Rahotanni sun ce Lucky Igbinedion ya hallara hedikwatar EFCC da ke Jabi, a Abuja da kimanin karfe 2:00 na ranar Alhamis, 11 ga watan Nuwamba, 2021.

EFCC ta sake taso keyar tsohon Gwamnan da ya taba shiga kurkuku ya fito saboda cin kudi
Bikin auren Diyar Lucky Igbinedion Hoto: @ChiefIgbinedion
Asali: Twitter

Har zuwa lokacin da ake samun wannan rahoto, ‘dan siyasar yana amsa tambayoyi a hedikwatar.

Lucky Igbinedion ba bakon EFCC ba ne

Reuters tace jim kadan da Lucky Igbinedion ya bar kan mulki a 2007, hukumar EFCC ta fara bincikensa, kuma ta gurfanar da shi a babban kotun tarayya da ke Enugu.

Lauyoyin EFCC sun yi nasarar daure tsohon gwamnan a gidan yari bayan Alkali ya same shi da laifin satar Naira biliyan 2.5 daga asusun gwamnatin jihar Edo.

A wancan lokaci, kotu ta ba Mista Igbinedion zabin maida kudi ko ya yi shekara shida a kurkuku. Alkali A. Abdu-Kafarati da yanke wannan hukunci ya rasu.

Kara karanta wannan

EFCC ta shiga kotu da tsohon Minista, wasu 4 saboda cin kudin Diezani Madukwe a zaben 2015

Meya faru a wannan karo?

Wannan karo ana zargin cewa tsohon gwamnan ya karbowa jihar Edo bashi, amma a karshe kudin suka kare wajen biyan bashin da wani kamfaninsu ya karba.

Mai magana da yawun bakin hukumar EFCC na kasa, Wilson Uwujaren, ya tabbatar da cewa tsohon gwamnan yana hannunsu, amma bai yi karin bayani ba.

Kudin da jami'an EFCC su ke zargin babban 'dan adawar da handama sun kai Naira biliyan 1.6.

Sulhu da 'yan IPOB?

Ministan shari'a na kasa, Abubakar Malami ya bar kofar yin sulhu da Shugaban IPOB, Nnamdi Kanu da Sunday Igboho a bude a lokacin da aka yi masa tambayoyi.

An kuma ji Malami ya samu lokaci ya maidawa Gwamnoni martani kan zargin da suke yi masa na biyar 'yan kwangila kudi cikin gaggawa daga asusun Paris Club.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng