Jinsi ba shamaki bane: Injiniya mace 1 cikin maza ta sanar da gwargwamayar da ta sha duk da maraicin ta
- Sau da yawa jinsi na iya zama shinge ga matan arewa a irin karatuttuka ko bangarorin da ake samun maza ba da yawa
- Zaman Maryam mace bai hana ta dagewa ta nema abinda ta ke so ba, ta kammala karatun ta a fannin injiniyancin wutar lantarki da na'ura mai kwalwalwa
- Duk da kalubalen da ta fuskanta na zaman ta mace cikin maza, matashiyar mai shekaru 22 ta ce ta samu karfin guiwa daga mahaifiyarta da taimakon abokan karatun ta
A makon da ya gabata ne wani hoto ya dinga yawo a kafafen sada zumunta na wata mace jaruma guda daya cikin maza injiniyoyi da suka kammala digirinsu a fannin lantarki da na'ura mai kwakwalwa a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria.
Legit.ng ta zanta da jarumar matashiyar mai suna Maryam Jibril mai shekaru 22 a duniya 'yar asalin jihar Taraba da ke arewacin Najeriya.
Kamar yadda Maryam ta bayyana, ta mika godiyarta ga Allah madaukakin sarki da ya bata damar kammala karatun ta duk da kuwa karatun an fi samun maza ke yin sa.
Maryam ta sanar da yadda ta dinga samun kira kan cewa hotunan ta suna yawo a kafafen sada zumunta daga 'yan uwa da abokan arziki.
Kallabin ta ce, babu shakka wadannan zaratan matasan mazan na ajinsu sun matukar taimaka mata a cikin shekaru 5 da suka yi tare suna karatu. Sun dinga bata karfin guiwa sosai duk da ta san abinda ta ke so kuma da kanta ta nemi irin karatun.
Sai dai ta jaddada cewa babu shakka al'amarin ba mai sauki ba ne. Ta yi kira ga mata matasa da ke son irin bangaren a karatu da su dage tare da bin abinda su ke so.
"Ga mata masu son irin karatun da nayi kada su bar jinsi ya zama musu shinge, su dage da addu'a, aiki tukuru tare da jajircewa, za su yi abubuwa masu tarin yawa da suke so.
"Ina fatan cigaba da karatuna bayan sakamakon karshe ya fito, ina fatan samun inda za a dauka nauyin karatuna domin yin digiri digir nan gaba," cewar Injiniyar.
Ta mika godiyar ta ga mahaifiyarta da ta tsaya mata duk da kuwa mahaifin ta ya rasu tana da karancin shekaru, kawun ta, abokan karatun ta wadanda ta ce sun matukar taimakawa wurin ganin ta kawo wannan mataki, malamanta 'yan uwanta, abokan arziki da sauran kawaye.
Kallabi tsakanin rawuna: Abubuwa 10 da ba a sani ba game da Arotile
A wani labari na daban, kallabi tsakanin rawuna, mace ta farko da ta zama matukiyar jirgin yaki a rundunar sojin saman Najeriya, Tolulupe Arotile, ta rasu sakamakon hatsarin mota a Kaduna.
Rundunar sojin saman Najeriya ta sanar da rasuwar Arotile a ranar Talata, sakamakon raunikan da ta samu daga hatsarin mota.
Baya ga zamanta mace ta farko matukiyar jirgin sama na yaki, akwai abubuwa da yawa ta yuwu ba a sani ba game da matukiyar jirgin saman.
Asali: Legit.ng