Asirin kuɗi: An kama wani mutum da ya haɗa baki da malamin addini mai shekaru 95 don kashe ɗan cikinsa
- Jami'an rundunar yan sanda a Enugu sun kama wani mutum da ake zargi da yin amfani da dan cikinsa don asirin kudi
- Yan sandan sun kuma kama wani fasto mai shekaru 95 da mutumin ya ce sun hada baki wurin aikata mummunan lamarin
- Bayan ya amsa laifin da ake zarginsa da aikatawa, mahaifin yaron ya fadawa 'yan sanda inda suka birne gawar yaron
Enugu - ‘Yan sandan jihar Enugu da ke kudu maso gabashin Najeriya, sun kama wani mutum bisa amfani da dansa don yin kudin bisa ruwayar Premium Times.
An kuma kama wani makahon fasto a jihar wanda ake zargin ya na da alaka da aikata laifin kamar yadda ‘yan sanda su ka ruwaito.
Premium Times ta bayyana yadda kakakin rundunar ‘yan sandan Enugu, Daniel Ndukwe, ya bayyana yadda lamarin ya auku ta wata takarda.
A takardar ta ranar Alhamis, ya bayyana yadda aka nemi dan mutumin mai shekaru 7 aka rasa a ranar 22 ga watan Oktoba, daga baya aka gane kudin jini mahaifinsa ya yi da shi.
Ndukwe ya ce bayan samun labarin batar yaron, ‘yan sandan su ka kama mahaifinsa, Onyishi Chidi mai shekaru 36 a ranar 6 ga watan Nuwamba a Coal Camp da ke Enugu.
Mahaifin ya amsa laifinsa
Ya kara da cewa:
“Chidi ya bayyana yadda ya aiwatar da ta’addanci, wanda bayaninsa ya kai ga kama wani makahon fasto, Okeke Eneokwor mai shekaru 95, wanda su ka yi aika-aikar tare.
“Ya kuma kai ‘yan sanda da wasu ma’aikatan lafiya zuwa wani rafi da ke Abakpa-Nike a Enugu, inda suka haka karamin rami su ka birne yaron.”
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Lawal Abubakar, ya umarci a aiwatar da bincike mai tsanani akan lamarin.
Abubakar ya umurci mazauna jihar da su kasance masu bin doka da kuma lura da ‘yan ta’adda. A cewarsa ya kamata su yi gaggawar kai rahoto ga ‘yan sanda idan su ka ga wata harkar ta’addanci.
'Yan sanda sun yi ram da wasu samari 2 bayan sun datse wa juna hannaye yayin kwasar dambe
A wani labarin, 'yan sanda sun yi ram da samari 2 bisa kama su dumu-dumu da laifin sare wa juna hannaye, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.
An ruwaito yadda ‘yan sandan su ka kama Adamu Mohammed da Bukar Audu, bayan sun datse wa juna hannaye yayin wani fada da su ka tafka a Garin Alkali, karamar hukumar Dapchi da ke jihar Yobe.
Premium Times ta bayyana yadda Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Dungus Abdulkarim, a ranar Litinin a Damaturu ya bayyana a wata takarda.
Asali: Legit.ng